Fashewar bututun mai ya kashe mutum 62 a Abiya- NEMA
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta sanar da mutuwar mutum 62 sakamakon fashewar bututun mai a jihar Abiya, wanda ya faru makon da ya gabata. Shugaban NEMA a shiyyar jihohin Imo da Abiya Mista Evans Ugoh ne ya sanar da hakan yayin ziyarar gani da ido. Ya kuma dora alhakin fashewar bututun […]
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta sanar da mutuwar mutum 62 sakamakon fashewar bututun mai a jihar Abiya, wanda ya faru makon da ya gabata.
Shugaban NEMA a shiyyar jihohin Imo da Abiya Mista Evans Ugoh ne ya sanar da hakan yayin ziyarar gani da ido. Ya kuma dora alhakin fashewar bututun kan rashin kula da bututun man da ba a yi wanda hakan ya janyo fashewar.