Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno
Yara mata uku sun rasu sakamakon fashewa3 wani gurneti da ake zargin na mayaƙan Boko Haram ne a yankin Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno
Gawa
Fashewar gurneti ya salwantar da rayukan yara mata uku a garin Pulka da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
A wani rahoto da ma’aikacin Sibiliyan JTF Buba Yaga ya fitar, ya ce ɗaya daga cikin ƙananna yaran suna wasa da gurnetin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, suka yi watsi da su a lokacin da gurnetin ya tashi da misalin ƙarfe 2:20 na ranar Alhamis.
An garzaya da yaran zuwa Babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Daga nan ne aka miqa gawarsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
- Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja
- Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja
Haɗaɗɗiyar tawagar ’yan sandan da suke tantance bama-bamai (EOD-CBRN), da dakarun Operation Hadin Kai, CJTF, da mafarautan yankin sun ziyarci wurin, inda suka gudanar da aikin share wasu na’urori.
Ba a samu ƙarin ko ɗaya ba, kuma an ayyana yankin a matsayin keɓantaccen wurin da za a kauce wa bi zuwa wani lokaci.
Hukumomin tsaron sun bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton abubuwan da suke zargi ga jami’an tsaro domin hana afkuwar irin wannan bala’i.