Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja
Hukumomi na gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.

Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara.
- Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba
- Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka.
Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun isa wajen domin ceto mutanen da abin ya shafa.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Babban Birnin Tarayya, ’Yan Sanda, da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun duƙufa wajen kai ɗauki.
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata an kai su Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa domin samun kulawar gaggawa.
Shirin Inganta Amfani da Gas (PCNG) na Fadar Shugaban Ƙasa, ya bayyana jimaminsa game da wannan hatsari.
Ya yi alƙawarin gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa tankar gas ɗin ta samu matsalar birki, wanda hakan ya haddasa fashewar tankin mai.
A cikin wata sanarwa, PCNG ya buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita har sai an kammala bincike.
Hakazalika, ya jaddada aniyarsa na tabbatar da aminci wajen amfani da CNG, tare da ɗaukar matakan hana aukuwar irin wannan hatsari a nan gaba.
Jami’an agaji sun ci gaba da aikin ceto da bayar da taimako ga waɗanda lamarin ya shafa, tare da ƙoƙarin shawo kan ɓarnar da gobarar ta haifar.