Fashewar tankar mai: Mamata sun ƙaru zuwa 170

Adadin mutanen da suka rasu a fashewar tankar man fetur ta kashe a Jihar Jigawa ya ƙaru zuwa 170, wasu sama da 60 na karbar magani

Fashewar tankar mai: Mamata sun ƙaru zuwa 170

Adadin mutanen da suka rasu a fashewar tankar man fetur ta kashe a Jihar Jigawa ya ƙaru zuwa 170 a yayin da wasu sama da  60 ke karbar magani.

Gwamnan jihar, Umaru Namadi, ta bayyana cewa har yanzu wasu mutanen ba su gano ’yan uwansu a cikin mamatan ba, saboda gawarwakinsu sun kone fiye da misali.

Gwamnan ya bayyana cewa sun gano adadin ne a yayin rangadin gani da ido da gwamnatin jihar ta gudanar tare da wakilan Gwamnatin Tarayya.

A ranar Alhamis ne Gwamnatin Kano ta bayar da gudummawar Naira miliyan 100 domin tallafa wa mutanen da ibtila’in ya ritsa da su.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da tallafin ne a yayin ziyarar jaje da ya kai wa Gwamna Namadi.

Abba wanda ya ce tallafi zai taimaka wajen kuɗaɗen jinyar marasa lafiya da kuma tallafa wa iyalan waɗanda abin ya rutsa da su.

Gwamnan Kano ya kuma jajanta wa al’ummar Jigawa bisa ibtila’in na garin Majia da ke Karamar Hukumar Taura.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu