Fashewar tukunyar gas yayi ajalin mutum 1, wasu sun jikkata a Neja

Ɗalibin ya rasu nan take bayan fashewar tukunyar gas ɗin.

Fashewar tukunyar gas yayi ajalin mutum 1, wasu sun jikkata a Neja

Wani ɗalibi mai suna Haji ya rasu, yayin da wasu mutum uku suka jikkata, bayan wata tukunyar gas ta yi bindiga a wajen wani mai gyaran taya a Minna, a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kusa da ofishin ’yan sanda na Kpakungu.

Mai gyaran tayar mai suna Mohammed da ɗansa, da wani ɗalibi sun samu munanan raunuka a lokacin da tukunyar ta fashe, yayin da Haji ya rasu nan take a wajen.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana, lokacin da mai gyaran tayar yake gyara wasu tayoyin manyan motoci.

Fashewar ta lalata shagonsa tare da rushe katangar wani gida da ke kusa da wajen.

Wani mazaunin yankin, Usman Mohammed, ya bayyana cewa ƙarar fashewar ta tayar da hankalin jama’a.

Ya ƙara da cewa an yi jana’izar marigayin Haji a maƙabartar Kpakungu.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce waɗanda suka an jikkata an garzaya da su asibiti.

Amma, abin takaici, ɗaya daga cikin ɗaliban ya rasu, yayin da sauran suke samun kulawa.