Fashewar wani abu ta kashe mutane a Katsina
Fashwar wani abu da ba a san ko mene ne ba ta halaka wasu mutane a kauyen Yammama da ke Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina. Abin ya fashe ne a daidai wurin da wasu manoma ke aiki a wata gona inda nan take wasu suka rasu, wasu kuma suka samu raunuka. “Na kirga gawarwaki […]
Fashwar wani abu da ba a san ko mene ne ba ta halaka wasu mutane a kauyen Yammama da ke Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Abin ya fashe ne a daidai wurin da wasu manoma ke aiki a wata gona inda nan take wasu suka rasu, wasu kuma suka samu raunuka.
“Na kirga gawarwaki shida bayan wasu biyar da aka kai asibiti, kuma jami’an tsaro sun killace wurin”, inji wani shaida, wanda ya ce mutanen da abin ya rutsa da su ‘yan kwadago ne a gonar.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu bayani game da adadin wadanda abin ya shafa a hukumance, kuma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ba ta kai ga yi wa wakilinmu bayani ba.