Fashin bankuna a Offa: ’Yan sanda sun kama karin mutum 12 da ake zargi
Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta kama karin mutum 12 da ake zargi da hannun a fashin bankunan da aka yi a garin Offa da ke Jihar Kwara a kwanakin baya. Kakakin Rundunar ta kasa Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Jimoh Moshood ya bayyana haka a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja. Ya bayyana […]

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta kama karin mutum 12 da ake zargi da hannun a fashin bankunan da aka yi a garin Offa da ke Jihar Kwara a kwanakin baya.
Kakakin Rundunar ta kasa Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Jimoh Moshood ya bayyana haka a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da cewa sun hada da: Adegoke Shogo mai shekara 29 da Kayode Opadokun mai shekara 35 da Kazeem Abdulrasheed mai shekara 36 da Azeez Abdullahi mai shekara 27 da Aledander Reuben mai shekara 39 da Jimoh Isa mai shekara 28 da Azeez Salaudeen mai shekara 20
Sauran su ne: Adewale Popoola mai shekara 22 da Adetoye Mufutau mai shekara 23 da Aminu Ibrahim mai shekara 18 da Richard Terry mai shekara 23 da kuma Peter Kuunfa mai shekara 25.
Tun farko dai ‘’yan sanda sun kama mutum tara kan zargi da hannu a fashi da makamin.
A ranar 5 ga Afrilu ne ’yan fashi da makamin suka kai hari ga bankuna biyar, inda a lokacin suka hallaka mutum 17 ciki har da ’yan sanda da wata mata mai juna biyu.
Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris bayan aukuwar lamarin ya bayar da umarnin a tura karin rukuni uku na ’yan sandan kwantar da tarzoma (PMF) da wani kakkarfan kwamitin bincike na ’yan sanda da kuma motoci masu sulke zuwa Jihar Kwara.
Moshood ya ce kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da kananan bindigogi kirar bareta guda biyu da harsasai masu rai guda 20 da wayoyin hannu guda hudu da layukan waya na wadanda fashin ya shafa wadanda wadansu daga cikinsu an kashe su a lokacin harin.
Ya ce wadanda ake zargin sun yi ikirarin irin miyagun ayukan da suka aikata a yayin fashin.
“A baya an taba bincikarsu tare da gurfanar da su a gaban kotu kan zargin fashi da makami da kasacewa cikin kungiyar asiri,” inji shi.
Ya kara da cewa tana dada kokarin kamo sauran wadanda ake zargi da suka gudu. “Rundunar ba za ta kwanta da sirdi ba, har sai ta zakulo duk masu hannu a wannan danyen aiki domin gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.