Fashin cikin teku ya addabi al’ummar Kudu maso Kudu

An tabka artabu tsakanin masu fashi kan teku da jami’an tsaro na ’yan sandan sojan ruwa da ke gudanar da sintiri a  gabar tekun Gini.Gabar, wadda ke tsakanin Jihar Kuros Riba da Jamhuriyar Kamaru, inda aka yi artabun, an yi nasarar kashe biyu daga cikin ’yan fashin, yayin da biyar daga cikinsu suka sami munanan […]

Fashin cikin teku ya addabi al’ummar Kudu maso Kudu
Fashin cikin teku ya addabi al’ummar Kudu maso Kudu

An tabka artabu tsakanin masu fashi kan teku da jami’an tsaro na ’yan sandan sojan ruwa da ke gudanar da sintiri a  gabar tekun Gini.
Gabar, wadda ke tsakanin Jihar Kuros Riba da Jamhuriyar Kamaru, inda aka yi artabun, an yi nasarar kashe biyu daga cikin ’yan fashin, yayin da biyar daga cikinsu suka sami munanan raunuka, amma suka afka ruwa suka gudu.
Lamarin ya faru ne ranar Talata yayin da wasu fatake suke cikin jirgin ruwa kan hanyarsu ta zuwa Kamaru, mafasan, cikin  jirgin ruwa mai gudun gaske suka kai musu hari suka datse su.
A cikin fataken ne wata mata da diyarta, wadda ba ta fi shekara daya ba, bayan ’yan fashin sun gano ta yi wa diyar kunzugu da kudin fataucin nata, sai suka kwance suka kwashe kudin, suka jefa ta cikin teku kuma suka harbe uwar.
DSP John Umoh, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kuros Riba ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin.
Wani dan kasuwa da ya bukaci a  sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, “Babbar matsalar ita ce idan ma ka bi ta karamar hanya ta Ikang, idan suka tare ku, wanda ba shi da kudi ko su amshe kayansa su lakada masa duka, ko kuma su dake ka su bar maka kayanka. Bambancin Najeriya da Kamaru ita ce su akwai lambobin waya da jami’ai masu sintiri suka bayar, wadda ba su ma  bukatar jin muryarka da zarar sun ga kira sun san akwai matsala kan teku,   nan take za su garzayo su kai dauki, wanda mu a nan Najeriya abin ba haka yake ba”. inji shi.
Mazauna jihohin Kudu maso Kudu na zama cikin firgici da rashin tabbas na tsaron rayukansu da dukiyoyi, “Saboda yanzu fashi ya yi yawa, daga ka ji an tare mutum an kwace masa abu kaza, sai ka ji an bi mutum har gida an yi masa yankan rago. Matsalar sukurkucewar tsaro ba Arewa kadai ke fama da ita ba”,  inji wani da Aminiya ta zanta da shi.