Fashola ya karrama ’yar sandar da ta kama ’yan fashi a Legas
Gwamnan Jihar Legas Mista Babatunde Raji Fashola ya karrama Saja Mercy John, wacce saboda jaruntarta ita kadai ta kama ’yan fashi biyu yayin da suka yi kokarin yi mata fashi a Jihar Legas. Yayin da yake jawabi a wurin bikin karrama ’yar sandar, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke unguwar Ikeja Legas, […]
Gwamnan Jihar Legas Mista Babatunde Raji Fashola ya karrama Saja Mercy John, wacce saboda jaruntarta ita kadai ta kama ’yan fashi biyu yayin da suka yi kokarin yi mata fashi a Jihar Legas.
Yayin da yake jawabi a wurin bikin karrama ’yar sandar, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke unguwar Ikeja Legas, Fashola ya karfafa mata gwiwar ci gaba da yin aiki tukuru.
Ya ce: “Bari na bayyana karara don kowa ya gane, na yaba wa aikin da kika yi kuma mutanen Legas sun yaba wa abin da kika yi. Ko daga ina kika zo, nan gidanki ne. Ina ganin daidai ne a ce saboda kin dauki Jihar Legas gidanki shi ya sa kika yi abin da ya dace, kin kama ’yan fashi biyu don mutane Legas su yi barci sosai.”
A nata jawabin, Saja Mercy John ta gode wa Gwamnatin Jihar Legas da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya sannan ta yi alkawarin ci gaba da yin aiki tukuru yayin da take gudanar da aikinta.
A ranar 10 ga watan Fabarairun bana, a yayin da Saja Mercy take tafiya a kan titin Orisunmibare da ke unguwar Egbeda sai wadansu ’yan fashi biyu suka tare ta inda suka yi kokarin kwace mata jakarta, ita kuwa ta yi ta maza ta rika bugawa da su har ta kai ta ci karfinsu, ta kwace bindigar da suka yi amfani da ita, da kwafson harsashi guda biyu, ta daure su, ta kai su ofishin ’yan sanda da ke kusa.
Ita dai Saja Mercy John, ’yar asalin karamar Hukumar Ekori da ke Jihar Kuros Riba ce. Ta shiga aikin ’yan sanda a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2000 kuma ta yi aiki a rundunar ’yan sandan kwantar da tarzoma mai lakabin Mopol 20 da ke yankin Ikeja daga shekarar 2004 zuwa 2012.
A yanzu tana aiki a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke yankin Ikeja a cikin jihar Legas.