Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo

Jami’in ya ce ana zargin direban motar da yin barci yayin da yake tuƙi, wanda shi ne ya haddasa hatsarin.

Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo

Aƙalla fasinjoji 12 ne suka ƙone ƙurmus har lahira a wani mummunan hatsari da ya auku a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Edo, Cyril Mathew, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.

Ya ce wata mota ƙirar Toyota Hiace ce ta yi karo da babbar tifa.

A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na asuba a ranar Asabar, a kusa da wani shingen sojoji da ke yankin Igueoviobo.

“Motar ta taso ne daga Zuba a Babban Birnin Tarayya tana kan hanyarta n zuwa Benin, amma ta yi karo da wata babbar tifa da ke kan hanyar zuwa Auchi.

“Duk fasinjojin da ke cikin motar sun rasa rayukansu,” in ji shi.

Mathew, ya ce ana zargin direban motar da gajiya yayin tuƙi, lamarin da ya sa ya fara barci a kan hanya, wanda hakan ya haddasa hatsarin.

Karon da motocin suka yi ya haddasa tashin wuta, lamarin da ya sanya fasinjojin zuka ƙone ƙurmus.

Sai dai direban babbar tifar da yaronsa sun tsira ba tare da sun ji rauni ba.

Kakakin ya shawarci direbobi da suke hutawa a duk lokacin da suka gaji domin gujewa aukuwar hatsari.