Fasinjoji 19 sun mutu a hatsarin mota a Oyo
Fasinjojin sun rasu ne sakamakon karo da motocin biyu suka yi da juna.
Aƙalla fasinjoji 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Oyo zuwa Ogbomoso a Jihar Oyo.
Hatsarin ya faru ne tsakanin wata farar mota ƙirar Toyota HIACE mai ɗaukar mutum 18 mai lamba NTT 522 ZY da wata baƙar mota ƙirar Toyota.
- Masu iƙirarin dakatar da Ganduje ba ’yan Jam’iyya ba ne —APC
- Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun mutu nan take yayin da mutum ɗaya da ya tsira aka kai shi asibitin Opabode da ke garin Oyo don kula da sa lafiyarsa.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Oyo, Joshua Adekanye, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon rashin bin dokokin hanya da tuƙi.
“A cikin fasinjoji 20 da ke cikin motocin biyu, 19 sun mutu nan take yayin da mutum ɗaya ya tsira.
“An kai gawarwakin waɗanda suka rasu babban asibitin Oyo. Direbobin motocin biyu na daga cikin waɗanda suka mutu nan take,” in ji shi.
Kwamandan, ya yi kira ga masu ababen hawa da suke tabbatar da lafiyar ababen hawansu da kuma dokokin hanya.