Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo
Hukumar FRSC ta tabbatar da cewar gudun wuce ƙima ne ya haddasa hatsarin.
Aƙalla fasinjoji 30 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Ore-Lagos a Jihar Ondo, bayan da wasu motoci biyu suka yi karo da juna sannan suka kama wuta.
Ganau, sun ce motocin suna tafiya zuwa Gabashin Najeriya ne, kuma suna gudun wuce ƙima kuma ga cunkoson ababen hawa a hanyar.
Hatsarin ya haddasa tashin wuta, inda mafi yawan fasinjojin suka ƙone ƙurmus.
“Motocin biyu sun yi karo, nan take suka kama da wuta,” in ji wata ganau, Misis Precision Oluwatuyi.
“Direbobin suna tafiya da gudu a hanyar da ba ta dace ba. Na ƙirga gawarwakin mutum 28 a waje , kuma wasu mutum biyu sun mutu a hanyarsu ta zuwa asibiti.”
Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Kwamanda Samuel Ibitoye, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.
Ya ce sakaci da gudun wuce ƙima ne ya haddasa hatsarin.
“Direbobi su tuna cewa nauyin da ke kansu shi ne su kai fasinjoji inda za su je lafiya, ba su jefa rayuwarsu cikin hatsari ba,” in ji shi.
“Fasinjoji su ma su dinga gargaɗin direbobi kan tuƙin ganganci don kaucewa irin waɗannan musifu.”
An kai gawarwakin mamatan Asibitin Ƙasa da ke Ore, yayin da sauran mutum biyu da suka jikkata ake kula da su.