Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

Tuni aka garzaya da fasinjojin da aka ceto zuwa asibiti domin ba su kulawa.

Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram.

Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram.

Sanarwar ta bayyana cewa motar na ɗauke da fasinjoji 44, wanda suka haɗa da manya 25 da yara 19.

Kakakin, ya ce wutar ta samo asali ne daga katifa da aka ɗaure a bayan motar, kusa da bututun fetur.

Mutum 10 da suka samu raunuka an garzaya da su asibitin Gwaram, yayin da aka ceto sauran fasinjojin ba tare da sun ji ciwo ba.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da Zuwairah Hassan mai shekaru 40, Fatima Hassan mai shekaru biyar.

Sauran sun haɗa da Iyatale Hassan mai shekaru uku da Halima Muhammad mai shekaru 10, dukkaninsu ‘yan ƙauyen Saldiga da ke Ƙaramar Hukumar Zaki, a Jihar Bauchi.