Fasinjoji sun firgita saboda lalacewar jirgin kasan Abuja

Fasinjojin da suka shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a karshen makon da ya gabata sun shiga fargaba yayin da jirgin ya samu matsala kusa da garin Jere inda aka rika samun wasu bata-gari na yin garkuwa da mutane a kwanankin baya. Jirgin wanda ya tashi da sanyin safiya daga tasharsa da ke unguwar […]

Fasinjoji sun firgita saboda lalacewar jirgin kasan Abuja

Fasinjojin da suka shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja a karshen makon da ya gabata sun shiga fargaba yayin da jirgin ya samu matsala kusa da garin Jere inda aka rika samun wasu bata-gari na yin garkuwa da mutane a kwanankin baya.
Jirgin wanda ya tashi da sanyin safiya daga tasharsa da ke unguwar Idu a Abuja da misalin karfe bakwai da minti uku na safe ya samu matsala har sau biyu.
Matsalar farko ta faru kafin ya tashi daga tasharsa ta Idu matsala ta biyu kuma ta faru ne a daidai garin Jere da ke jihar Kaduna.
Wakilinmu ya gano cewa injiniyoyin jirgin sun kwashe kimanin mintina 20 kafin su gyara matsalar da jirgin ya samu a garin Jere inda hakan ya kara sanya fasinjojin jirgin cikin fargaba. Matalsar ta auke da misalin karfe takwas da minti biyu amma an gyara jirgin da misalin karfe takwas da minti 22. Hakan shi ne karo na biyu da jirgin yake gamuwa da matsala a cikin makonni biyu.
Sai dai jami’an ma’aikatar sufurin jirgin kasa ta NRC sun sanar da fasinjojin cewa za su gyara jirgin cikin minti biyu kacal amma sai da aka dauki kimanin mintina 20 kafin a shawo kan matsalar.