Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Maitama don ba su kulawa.

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

Wasu rahotanni sun bayyana cewar fasinjoji da dama sun jikkata, bayan da wata tankar mai ta yi bindiga da yammacin Litinin a kan titin Shehu Shagari da ke yankin Maitama a Abuja.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:40 na yamma kusa da ginin ofishin Jakadancin Birtaniya.

Wani ganau, Saminu Sani, ya ce wutar da ta tashi yana kai wa tsayin hawa na huɗu na benen ginin Ofishin Jakadancin Birtaniya, lamarin da ya sanya direbobi barin motocinsu domin neman tsira.

Lamarin ya haddasa cunkoso mai yawan gaske a hanyoyi guda huɗu da ke haɗa Kasuwar Manoma, Otal ɗin Nicon Hilton, hedikwatar MTN, da kuma Chicken House.

Wani jami’in lafiya a Asibitin Maitama, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewar an kawo waɗanda suka jikkata don ba su agajin gaggawa.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira sun ce direban tankar ya tsere daga wajen jim kaɗan bayan tankar ta kife a ƙasa.

Rabon Awaki bai dace da Gwamnan Kano ba — Jaafar Jaafar

An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano

’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe

Gwamnati ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar titin Kano zuwa Abuja