Fasinjoji sun jirkita jirgin kasa don ciro karfar dan uwansu da ta makale a Austiraliya
A Yammacin Austiraliya, can a birnin Perth, fasinjoji suka yunkura don jirkita jirgin kasa saboda su ciro kafar wani fasinja da ta makale. Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa daruruwan mutane ne suka hada karfi wajen cicciba jirgin, a ranar Larabar da ta wuce, don su ciro kafar fasinja da ta makale, don […]
A Yammacin Austiraliya, can a birnin Perth, fasinjoji suka yunkura don jirkita jirgin kasa saboda su ciro kafar wani fasinja da ta makale. Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa daruruwan mutane ne suka hada karfi wajen cicciba jirgin, a ranar Larabar da ta wuce, don su ciro kafar fasinja da ta makale, don haka hukumomin kasar suka yaba musu, har suka yi wa al’amarin lakabi da “karfin mutane.”
Da farko dai an umarci fasinjojin ne da su koma gefe guda, ta yadda za su tattara nauyinsu wuri guda, ta yadda idan jirgin ya dan karkata sai a ciro kafar fasinjan, wanda wata jaridar The West ta kasar Austireliya ta bayar da sunansa a matsayin Nick. Da wannan dabara ta ki cin nasara, sai aka umarci fasinjojin da su sauka daga cikin jirgin kasan, inda mutum 50 daga cikinsu suka hada karfi wajen jirkita jirgin, ta yadda mutumin zai iya zare kafarsa.
“Wannan shi ne karo na farko da aka taba ganin wani al’amari irin wannan,” a cewar mai Magana da yawubn Kamfanin safara na Transperth, Claire Krol, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Kamfanin Transperth ya bayyana cewa jami’an kula da lafiya sun yi wa mutumin magani, sannan ya shiga jirgin an ci gaba da tafiya tare da shi. “Sakamakon wannan al’amari dai nasara ce ga mutumin da matsalar ta aukawa, amma babban abin farin ciki, shi ne, yadda kowa da kowa ya hada karfi a cikin al’umma, inji Krol.