Fasinjoji sun koka kan karin kudin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Ministan sufuri ya ce gwamnati ba za ta dauki asara ba, sai dai ina so ake ya rufe tashoshin

Fasinjoji sun koka kan karin kudin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Daya daga cikin sabbin jiragen kasa na hanyar Warri-Itakpe

Fasinjoji sun koka kwarai kan karin kudin jirgin kasa da aka yi daga Abuja zuwa Kaduna.

Wakilinmu da ya ziyarci tashar jirgin kasa da ke Idu a Abuja, ya ce babu fasinjoji sosai saboda an ninka kudin tikitin jirgin.

Manajan gudanarwar hukumar jirgin kasa, Victor Adamu, ya ce juye biyu na fasinjoji farko da suka dauka mutum 679 ne.

“Da karfe bakwai na safe, daukar farko daga Idu zuwa Kaduna mun samu fasinja 396, sai tafiya ta biyu mun dauki fasinja 283.

“Daga Kaduna zuwa Abuja, dibar farko da karfe 8:45 na safe mun samu fasinja 94 sai a dauka ta biyu muka samu 75”, inji manajan.

Jirgin kasa ya dawo aiki ne ranar Laraba 28 ga Yuli, 2020 bisa tsarin bayar da tazarar da yin feshin magani don kariya daga COVID-19 wadda ta sa aka rufe tashoshin na tsawon watanni.

Gabanin bude tashoshin, Ministan Sufuri Rotimi a Amaechi ya sanar da ninka farashin tikiti tare da wajabta bin matakan kariya ga dukkanin fasinjoji.

‘Hawa jirgin zai gagari talaka’

Fasinjoji da suka hau jirgin baya dawo da jigilar sun koka kwarai da karin kudin jirgin inda wasu suka ce babu tausayi ciki.

Amma kuma sun yaba wa hukumar jirgin kasa wajen bin dokokin kariya na COVID-19.

Wata fasinja, Mairo Hassan ta ce karin da ka yi zai sa shiga jirgin ya gagari ‘yan Najeriya masu karamin karfi.

“Annobar COVID-19 ta karya tattalin arzikin mutane. Ka duba, mutane ba su cika ko tarago daya ba saboda tsadar jirgin.

“A da babu masaka tsinke idan ka zo nan. Ya kamata a duba dai”, a ganawarta da wakilinmu.

Jirgin zai gagari talaka

A nata ra’ayin, Zeenat Ahmed, cewa ta yi bai kamata gwamnati ta kara kudin jirgin haka ba.

“Maimakon a ninka kudin, kamata ya yi gwamnati ta biya rabi, fasinja su biya rabi.

“Kafin wannan lokacin, ina biyan N2,500 a taragon manyan mutane, amma yanzu sun mayar da shi N6,000.

“Ga shi kuma hanyar ba tsaro, fasinja za su so su biya ko nawa amma babu kudi yanzu”, inji ta.

‘Gwamnati ba za ta dauki asara ba’

Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, a ziyarara ta ganin yadda ake bin kaidojin COVID-19 ya ce gwamnati ba za ta dauki asarar kujerun da ake tsallakewa ba a cikin jirgin don bayar da tazara.

“An samu karin kudin ne saboda a samu kudin tafiyar da harkar jirgin.

“Idan mutane ba sa so sai mu bari, amma dole ne a kara kudin jirgin in har ana so mu yi aiki.

“Abun da ya fi komai muhimmaci shi ne lafiyar mutum”, inji Amaechi.