Fasinjoji sun maƙale bayan jiragen sama sun katse jigila a Najeriya

Fasinjojin sun maƙale bayan da kamfanonin jiragen sama suƙa taƙaita zirga-zirga a cikin gida a Najeriya

Fasinjoji sun maƙale bayan jiragen sama sun katse jigila a Najeriya

Fasinjoji a faɗin Najeriya sun shiga tasku, bayan da kamfanonin jiragen sama suka dakatar da zirga-zirga.

Hakan ya jefa mutane da dama cikin halin rashin tabbas, duba da ƙarancin jiragen da ke zirga-zirga, musamman daga Legas zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Legas.

Fasinjoji da dama ba su samu damar yin tafiya ba ranar Talata a sakamakon wannan matsala.

Jirgin Max Air na ƙarfe 6 na yamma daga Legas zuwa Abuja ya cika gaba ɗaya amma abun mamaki bai tashi ba.

Haka kuma, jiragen Air Peace na ƙarfe 6:30 da 8:30 na yamma sun bayyana cewar ba su da sauran kujeru a ƙasa.

Wannan lamarin ya bar fasinjoji da dama cikin kaɗuwa da kuma rashin tabbas.

Wani ma’aikacin jirgin sama ya bayyana cewa, “Akwai ƙarancin jiragen sama, kuma mutane da yawa suna son yin tafiya.”

Wani ma’aikacin jirgi da ya nemi a sakaya sunansa ya ƙara da cewa kamfanonin jiragen sama na rage yawan tashi don kauce wa matsaloli.

Masanin harkokin sufurin jiragen sama, Mista Olumide Ohunayo, ya ce wannan yanayi ba zai rasa nasaba da sabbin dokokin kare haƙƙin masu amfani da jiragen sama ba.

Ya ce, “Wasu daga cikin jiragen da aka ce sun cika, an soke su ne ko kuma ba za su tashi ba.”

Ya ƙara da cewa kamfanonin jiragen sama suna ƙara taka-tsantsan wajen tsara jadawalin tashinsu don guje wa matsaloli.

Yayin da lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke ƙaratowa, Mista Ohunayo ya yi gargaɗin cewa kuɗin tikitin jirgi zai iya tashi saboda ƙarancin jiragen.

Kazalika, ya yi kira ga hukumar kula da sufurin jiragen sama da ta bai wa ƙananan kamfanoni lasisi don samun damar shiga harkar wanda hakan na iya rage matsalolin da ake fuskanta.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja