Fasinjoji sun yi zanga-zanga kan jinkirin tashin jirgin Max Air a Kano
Jinkirin tashin fasinjoji daga jiragen cikin gida, ya zama ruwan dare a Najeriya.
Wasu fusatattun fasinjoji a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da ke Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan tsaikon da jirgin Max Air ya yi a yayin da suke shirin zuwa Legas.
Jirgin na kamfanin Max Air mai lamba (VM1645) wanda aka shirya zai tashi da farko da karfe 1:00 na rana, sai aka jinkirta lokacin tashinsa ba tare da an sanar da fasinjojin ba, inda suka zauna na kusan sa’o’i biyar.
- Mutum 3 sun shiga hannu kan yunkurin tada tarzoma a Kano
- Gwamnan Oyo ya rufe kamfanin hakar ma’adinan ’yan China
Rashin fitar da sanarwa daga kamfanin ya kara dagula lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali a bangaren sufurin cikin gida.
Jinkirin tashin jirgin saman cikin gida a Najeriya ya zama ruwan dare.
A lokuta da dama fasinjoji kam asara musamman ga ma’aikata ko ‘yan kasuwar da suka shirya wa halartar wani taron aiki ko na kasuwanci.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wani jami’in kamfanin Max Air, sai dai ya ce ba shi da izinin yin martani a madadin kamfanin.