Fassara Fina-finan Indiya Zuwa Hausa: Jan hankali ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano
daya daga cikin nada-nade da Gwama Ganduje ya yi a Kano da suka zama zakaran gwajin dafi, shi ne na kujerar da ya dora ka na shugabancin Hukumar Tace Finai-finai ta Jihar Kano. Ba don wani abu ba sai dai don ganin cewa kai dan cikin gida ne a wannan harka ta finai-finan Hausa a […]
daya daga cikin nada-nade da Gwama Ganduje ya yi a Kano da suka zama zakaran gwajin dafi, shi ne na kujerar da ya dora ka na shugabancin Hukumar Tace Finai-finai ta Jihar Kano. Ba don wani abu ba sai dai don ganin cewa kai dan cikin gida ne a wannan harka ta finai-finan Hausa a wannan kasa tamu.
Duk da cewa wasu manazarta sun yi dan korafi na ganin cewa nada ka zai kawo rabuwar kai a masana’antar, ganin irin rabe-raben kai da kuke da shi a Kannywood. Wasu kuma suna ganin cewa a dauko wanda ya san harkar daga waje shi ne mafi cancanta amma ni dai a tawa fahimtar, dauko ka zai ba duniyar harkar fim wata damar, ganin danta ne yake shugabantar wannan hukuma. Domin ko ba komai, ka san irin matsalolin da suke fuskantarku da kuma ci gabanku, don kuwa Bahaushe na cewa mai daki shi ya san idan ruwa yake mai yoyo a daki. Allah Ya taya riko.
Babban makasudin rubuto maka wannan wasika shi ne, domin karantar wani furici naka da na yi kan masu fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa, cewa hukumarka ta hana sayar da su a kasuwa. Duk da yake na yi kokari na ga dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, na rasa samu, amma ko dai ma mene ne, na san dai dokar da ta kafa ku ba ta yi bayani kan fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa ba, domin lokaci da aka yi dokar ba a yi tunanin cewa za a fara fassara fina-fianan Indiya zuwa Hausa ba. Saboda haka doka ba ta ba ka damar ka hana fasara fim na Indiya zuwa Hausa ba a hukumance. Amma a ra’ayinka za ka iya daukar wannan dama don kana matsayin shugaban wannan hukuma kuma mai kishi da wannan fassara; ganin cewa tana kawo maku koma baya wurin sayar da fina-finan Hausa.
Bincike ya nuna cewa a duniya, fassara fim zuwa wani harshe domin fahintar ’yan kasar ta hanyar da ake kira (Saka Murya)ba laifi, da sharadin cewa ba sakon fim din da aka fassara aka canza ba. Sai dai shi mai fim din, wato mai hakkin mallaka, shi ne yake da ikon fassara fim din a rubuce, abin da ake kira da subtitling. Fassara kalaman fim a rubuce jikin fim, doka ce mai karfi a duniya, amma fassara fim ta hanya saka masa yare na daban domin fahimtar ’yan kasar da aka fassara fim din domin su, hakki ne na hukumar kasa, ta gani cewa ba a fassara fim din ta wata hanya da za ta fita daga ainihin fim din da aka fassara shi ba.
Saboda haka ni a shawarata, ina ganin abin da ya d ace da kai shugaban hukumar nan ka yi, shi ne ka yi wani kwamiti mai karfi a kan fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa, domin ganin ana samun gamsasshiyar fassara; ba irin wannan da ake yi ba. Dokar hukumar tana da ikon ta tsaftace harkar amma ba ta hana ba.
Matsala ta biyu da nake da korafi a kai, ita ce yadda ake samun wasu korafe-korafe a kan irin fina-finai da suke fitowa, da ba su da wani amfani ga masu kallo, sai ma badala da irin wadannan fina-finai suke koyarwa ga matsa da sauran al’umma. Ya dai kamata ka duba ka sake tsara dokokin duba fim kafin a ba shi izinin fitowa. Lokaci ya yi da za mu daina dauka da fahimtar cewa duk mutumin da ya yi, fim dole ya fito da shi kasuwa. Ya kamata ka rika kiran taron nazari da tantance duk wani fim da aka kawo wa hukumarka, don jin ra’ayin masana da manazarta da kuma ’yan kallo, kafin a saki duk wani sabon fim da aka shirya kasuwa.
Da fatan za ka duba wannan wasika tawa cikin ilimi don a samu ci gaba a wannan harka. A guji ’yan baka, masu ganin cewa dama tun da farko da haushin masu fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa ka shigo hukumar.