Fassara: Ma’anarta da matakanta

A wannan mako Aminiya ta kalato yadda ake fassara ce daga wani harshe zuwa wani harshen tare da misalai daga kundin masana daban-daban domin amfanin mai karatu da daliban ilimi. Masana suna bayyana fassara da cewa ita ce juyawa ko sauya wata magana daga wani harshe zuwa wani. Wannan magana tana iya zama baka da […]

Fassara: Ma’anarta da matakanta

Marigayi Alhaji Abubakar Imam Uban masu fassara a ilimin boko

A wannan mako Aminiya ta kalato yadda ake fassara ce daga wani harshe zuwa wani harshen tare da misalai daga kundin masana daban-daban domin amfanin mai karatu da daliban ilimi. Masana suna bayyana fassara da cewa ita ce juyawa ko sauya wata magana daga wani harshe zuwa wani. Wannan magana tana iya zama baka da baka ko rubutacciya zuwa rubutu, ko kuma daga rubutu zuwa maganar baka. Misali, idan aka faɗi magana da Hausa, kamar “Ado mutumin kirki ne,” sai kai ka juya ta zuwa Ingishi ka ce, “Ado is a generous person”. To, fassara ta samu amma ta baka da baka. Ko kuma a rubuta “Haza kitabun,” kai kuma ka juya ta zuwa “Wannan littafi ne.” A nan ma an yi fassara amma rubutacciya daga Larabci zuwa Hausa:

Ma’anar Fassara

Masana sun ba ta ma’ana ta, fasahar mayar da wani abin da aka faɗa ko aka rubuta daga wani harshe zuwa wani ba tare da canja ma’anarsa ba. (Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa, 1992; Sani, Muhammad da Rabeh, 2000).

Rabe-Raben Fassara

An raba fassara zuwa kashi biyu:

  1. Fassarar kai-tsaye: Fassara ce da mai yin ta yake fassara abu ba tare da canja tsari, salo da kuma ma’anar abin ba. A nan ana fassara abin ne yadda yake a wancan harshen. Fassarar da ta shafi addini, wato idan za a fassara littattafan addini, kamar Hadisi ko Ƙur’ani da sauransu, ko kuma za a yi fassara a fagen kimiyya, to ba a canja ma’anar kalmar. Misali, idan za a fassara “Awwalu ma yajibu,” sai a ce “Farkon abin da ke wajaba.” Wannan salon fassara shi ake kira fassara marar ’yanci.
  2. Fassara mai ’yanci: Fassara ce da mai yin ta ke da cikakkiyar dama ta fassara abu a yadda ya fahimce shi, amma ba tare da ya canja manufa ba. Wato ita wannan fassarar ana karanta abin ne sannan a juya shi yadda aka fahimce shi. Ana yin wannan fassara a cikin abubuwan da suka shafi labari, jawabi, wasanni da makamantansu.

Rukunan Fassara

Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yaraduwa (1992), sun zayyana abubuwa huɗu a matsayin rukunan fassara kamar haka:

  1. Naƙaltar harsuna: Abin da ake nufi a nan shi ne cewa dole ne mai yin fassara ya san harsunan da zai yi wa fassara, sannan ya yi musu kyakkyawar fahimta; wato ya san harshen da aka yi magana da shi, sannan da wanda zai juya maganar zuwa cikinsa. Misali, wanda zai riƙa yin fassara daga Ingilishi zuwa Hausa dole ya fahimci harshen Hausar da kuma Ingilishi, fahimta kuma ta haƙiƙa.
  2. Sanin al’adu: Dole ne mai yin fassara ya san al’adun waɗanda zai fassara maganar zuwa harshensu. Misali, idan mai fassara zai yi fassara zuwa harshen Hausa, to dole ya san al’adun Hausawa, sani kuma ba na shanu ba.
  3. Bincike: Dole ne mai yin fassara ya kasance mai zurfafa bincike a fannonin ilimi dan ya samu isassun kalmomin da za su taimaka masa wajen yin kyakkyawar fassara.
  4. Ƙamus: Dole ne mai yin fassara ya mallaki ƙamus na harsunan da yake yin fassara a cikinsu.

Matakan yin fassara

  1. Karatu: Karatu a nan yana nufin mai yin fassara ya karanta abin da zai fassara, karatu na haƙiƙa. Zai yi kyau mai fassara ya karanta abin da zai fassara, sannan ya sake maimaitawa har sai ya fahimci abin da zai fassara ɗin sosai.
  2. Gwaji: Bayan an karanta kuma sai a gwada yin fassarar. Ana iya yin haka ta hanyar yanko wani ɓangare na abin da aka karanta a fassara shi, sannan a yi nazarinsa a ga yadda abin yake, abin ya dace ko kuwa.
  3. Aiki: Mataki na ƙarshe kuma shi ne a shiga aikin fassarar gadan-gadan.

Abubuwan lura wajen yin fassara

Yana da matuƙar muhimmanci mai fassara ya kiyaye waɗannan abubuwa:

  1. Yin amfani da sassauƙar Hausa. Abu ne mai kyau mai yin fassara ya yi amfani da sassauƙar Hausa wacce za ta yi sauƙin fahimta a wajen mai karatu.
  2. Fassarar Kalma da Kalma: Akwai fuska biyu dangane da wannan gaɓa. An so yin fassarar kalma da kalma ko jimla da jimla a fagen addini. Ba a son yin fassarar kalma da kalma a yanayin fassara labari da makamantansa. Wato ke nan, idan za a yi fassarar kai-tsaye, to, ana yin ta ce ta hanyar kalma da kalma. Idan kuma fassara mai ’yanci ake yi, to, fassarar kalma da kalma, ko jimla da jimla abar ƙyama ce.
  3. Gauraye: Cakuɗa ƙarya da gaskiya a cikin fassara, abu ne da bai dace ba, kada ka aikata!

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare, Littafi na Uku. Unibersity Press PLC, Ibadan-Nigeria da kuma shafin Rumbun Ilimi.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano