Fassarar Sheikh Is’hak Yunus
Babi na Bakwai: Alkawarin tsaro (bayar da kariya) ga Abubakar a lokacin Manzon Allah (SAW): 34. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu ya ce, dan Hisham ya ce, Urwata dan Zubair ya ba mu labari cewa: “A’isha matar Annabi (SAW- Allah Ya yarda da ita), ta […]
Babi na Bakwai: Alkawarin tsaro (bayar da kariya) ga Abubakar a lokacin Manzon Allah (SAW):
34. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu ya ce, dan Hisham ya ce, Urwata dan Zubair ya ba mu labari cewa: “A’isha matar Annabi (SAW- Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Babu abin da na fi kiyayewa face dai na iske iyayena biyu suna bauta wa Allah yadda ya dace da Musulunci. Kuma babu wani yini da zai shude face Manzon Allah (SAW) ya ziyarce mu da safe ko da yamma. Lokacin da aka jarabci Musulmi da yawan cutarwa, sai Abubakar ya fita yana mai nufin hijira zuwa Habasha, ya fara tafiya har sai da ya isa Barka Algimad sai dan Daginat ya iske shi lokacin shi ne shugaban Alkaryan. Ya ce, “Ina kake nufin tafiya ya Ababakar? Sai Abubakar ya ce, mutane ne suka fitar da ni, don haka nake son in kaura zuwa wata kasa don in bauta wa Ubangijina. dan Daginat ya ce, “Lallai mutum kamarka bai kamata ka fita ko a fitar da kai ba. Domin lallai kai kana taimakon mara shi, kuma kana sadar da zumunci, kana daukar nauyin wahalar mutane, kana saukar da bako. Kana kuma taimako wajen kawar da musibu bisa gaskiya. Lallai ni na dauki alkawarin tsare ka (ba ka kariya), ka koma ka bauta wa Ubangijinka a garinka. Sai dan Daginata ya hau tare da Abubakar suka koma ya kewaya da shi cikin manyan kafiran kuraishawa ya ce musu: “Lallai Abubakar bai fita, kuma ba a fitar da irinsa. Shin za ku fitar da mutum wanda yake taimakon mara shi, yana sadar da zumunci yana daukar nauyin mutane, yana saukar da bako yana taimako wajen gusar da musibu bisa gaskiya! Sai kuraishawa suka zartar da makwabtakar Abubakar bisa alkawarin dan Dagina, suka amintar da Abubakar. Sai suka ce, wa dan Daginat ka umurci Abubakar ya rika bauta wa Ubangijinsa a cikin gidansa. Ya yi Sallah ya karanta abin da ya so, kada ya cutar da mu da wannan, kuma kada ya rika daukaka murya da haka, domin mu lallai muna jin tsoron kada ya fitini ’ya’yanmu da matanmu da haka. Sai dan Daginat ya fazi haka ga Abubakar, sai Abubakar ya rika bauta wa Ubangijinsa a cikin gidansa, bai daukaka murya da Sallah, ko wajen karatu face a cikin gidansa. Sai Abubakar ya yi tunanin gina masallaci a cikin farfajiyar gidansa ya bayyana yana Sallah cikinsa, yana karatun Alkur’ani, sai matan mushirikai suka rika taruwa suna kewaye da shi suna kallo na mamaki. Saboda Abubakar ya kasance mai yawan kuka bai iya tsare hawayensa lokacin karatun Alkur’ani. Sai manyan kafiran kuraishawa suka firgita da haka, suka aika zuwa ga dan Daginat ya zo gare su, suka ce masa: “Lallai mun yi alkawarin tsare Abubakar ne bisa ya bauta wa Ubangijinsa a cikin gidansa, to ya ketare wannan ya gina masallaci a cikin gidansa, kuma yana rika daukaka muryarsa a Sallah da karatu. Kuma muna jin tsoron kada ya fitini ’ya’yanmu da matanmu don haka ka tafi gare shi, ka sanar da shi cewa: “Idan yana son ya ci gaba da bautar Ubangijinsa a cikin gidansa, to ya ci gaba. Idan ba haka yake so ba, ya ki yarda face sai ya rika daukaka murya to ka neme shi da ya warware alkawarin da ka yi masa na amana, domin muna jin tsoron kada mu ha’ince ka cikin haka. Kuma ba za mu iya barin Abubakar bisa daukaka muryar nan ba.” A’isha ta ce: “Sai dan Daginat ya je ga Abubakar ya ce, “Lallai ka san abin da na kulla alkawari shi a kanka, ko dai ka takaita bisa ga haka (Sallah cikin gida da rashin daukaka murya), ko kuma ka mayar (warware) mini da alkawarin da muka yi, domin ni, ban son Larabawa su ji cewa na yi ha’inci ga wani mutum da na kulla alkawari da shi.” Abubakar ya ce, “Na warware alkawarina da kai, na nemi tsarewa daga Allah da na Manzon Allah (SAW) a yinin yau cikin garin Makka. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika an nuna mini gidajenku na hijira (kaura), kuma na wata kasa mai gishiri mai yawan dabinai a tsakanin tsaunuka biyu wato Harrat biyu. Ana nan haka wanda ya yi hijira ya yi hijira zuwa Madina lokacin da Manzon Allah (SAW) ya ambaci haka. Wasu suka kaura Madina daga wadanda suka yi hijira zuwa Habasha. Abubakar ya shirya yana mai nufin hijira. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, ka saurara! Lallai ni, ina kaunar za a mini izini, sai Abubakar ya ce: “Shin kana kaunar haka! Uwata da Babana fansa ne gare ka? Ya ce, “Na’am, sai Abubakar ya tsare kansa ga Manzon Allah (SAW) don ya abuce shi, ya tanadi abincin rakuma biyu da suka kasance gare shi, na ganyen samur har na wata hudu.”