Fassarar Sheikh Is’hak Yunus 02
Babi na Sittin da Biyar: Azumin Ranar Arfa: 448. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Malik ya ce, Salim ya ba ni labari ya ce, Umair bawan Ummul Fadal ya ba mu labari cewa: “Lallai Ummu Fadal ta ba shi labari -Hawwala Sanad- ya ce, Abdullahi dan Yusuf ya […]
Babi na Sittin da Biyar: Azumin Ranar Arfa:
448. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Malik ya ce, Salim ya ba ni labari ya ce, Umair bawan Ummul Fadal ya ba mu labari cewa: “Lallai Ummu Fadal ta ba shi labari -Hawwala Sanad- ya ce, Abdullahi dan Yusuf ya ba mu labari ya ce, Malik ya ba mu labari daga Abu Nadir bawan Umar dan Ubaidullahi daga Umair bawan Abdullahi dan Abbas daga Ummul Fadal ’yar Harisa cewa: “Lallai wasu mutane sun yi musu a wurinta Ranar Arfa game da azumin Annabi (SAW) a ranar. Wasu suka ce: “yana azumi, wasu kuma suka ce, “Ba ya azumi.” Sai (Ummiul Fadal) ta aika masa da gorar nono yana tsaye a kan rakumarsa, ya sha shi (nonon).”
449. An karbo daga Yahya dan Sulaiman ya ce: “dan Wahab ya ba mu labari, -ko ya ce, an karanto daga gare shi- ya ce, Amru ya ba ni labari daga Bukair daga Kuraib daga Maimuna (RA), cewa: “Lallai mutane sun kai kuka game da azumin Annabi (SAW) a Ranar Arfa, sai ta aika masa da kokon madara, yana tsaye a matsayinsa ya sha mutane na dubinsa (kallonsa).”
Babi na Sittin da Shida: Azumin Ranan Sallar Azumi:
450. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Abu Ubaida bawan dan Azhar ya ce; “Na halarci Idi tare da Umar dan Khaddab (RA) sai ya ce: “Wadannan yini biyu Manzon Allah (SAW) ya hana yin azumi a cikinsu. (1) Ranar Buda Bakinku (Sallah) na azumi. (2) Ranar cin Layyarku.” Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, dan Uyainata ya ce, “Wanda ya ce, bawan dan Azhar hakika ya dace, wanda ya ce, “Bawan Abdurrahman dan Auf shi ma lallai ya dace da (sunan).”
451. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Amru dan Yahya ya ba mu labari daga Babansa daga Abu Sa’id (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya hana game da yin azumin Ranar Sallar Azumi da Ranar Sallar Layya, kuma ya hana kurman yafe (daurin tufafin Jahiliyya), kuma ya hana mutum ya yafa tufa daya, kuma ya hana Sallar Nafila a bayan Sallar Safiya da bayan Sallar La’asar.”
Babi na Sittin da Bakwai: Azumin yinin Layya:
452. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga dan Juraij ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari daga Adda’u dan Mina’u ya ce, “Na ji shi yana ba da labari daga Abu Huraira (RA), ya ce: “An hana game da yin azumin ranaku biyu da ciniki biyu. Azumin Ranar Sallar Azumi da Sallar Layya. An hana cinikin Mulasamat (shafa ba dubi) da cinikin Munbazat (jefo mini naka in jefa maka nawa).”
453. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Mu’azu ya ba mu labari ya ce, dan Aunu ya ba mu labari daga Ziyad dan Jubair ya ce, “Wani mutum ya zo ga dan Umar (RA), sai mutumin ya ce: “Ya yi alwashin azumi yini daya,” ya ce, “Ina tsammaninsa, ya ce, “Yinin Litinin sai ya dace da Ranar Idi.” Sai dan Umar ya ce, “Allah Ya yi umarni da cika alwashi. Amma Annabi (SAW) ya hana game da azumin wannan yini.”
454. An karbo daga Hajjaju dan Minhal ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Malik dan Umair ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Sa’idul Khudri (RA), wanda ya kasance ya yi yake-yake tare da Annabi (SAW) har sau goma sha biyu, ya ce: “Na ji abubuwa hudu daga Annabi (SAW) sun ba ni sha’awa: (1) Kada mace ta yi tafiyar yini biyu face tare da mijinta ko muharraminta (danginta). (2) Babu azumi a cikin yini biyu, Sallar Azumi da na Layya. (3) Kuma babu Sallah a bayan Sallar Safiya har sai rana ta bullo ko bayan La’asar har sai rana ta buya. (4) Kuma kada wani mutum ya kunsa kayan tafiya ziyara ga kowane masallaci face Masallatai Uku, Masallacin Harami; Masallacin Aksa (kudus) da Masallacina wannan.”