Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA:Idan mai azumi ya ci ko ya sha da mantuwa. Adda’u ya ce, “Idan ya shaki ruwa sai ya shiga makoshinsa babu laifi idan ya kasa mayar da shi.” Alhasan ya ce: “Idan kuda ya shiga makoshinsa (mai azumi) babu komai a kansa.” Alhasan da Mujahid suka ce, “Idan mutum […]
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA:
Idan mai azumi ya ci ko ya sha da mantuwa. Adda’u ya ce, “Idan ya shaki ruwa sai ya shiga makoshinsa babu laifi idan ya kasa mayar da shi.” Alhasan ya ce: “Idan kuda ya shiga makoshinsa (mai azumi) babu komai a kansa.” Alhasan da Mujahid suka ce, “Idan mutum ya tara da matarsa da mantuwa babu komai a kansa.”:
393. An karbo daga Abdan ya ce: “Yazid dan Zura’u ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, dan Sirin ya ba mu labari daga Abu Huaraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Daga Annabi (SAW) ya ce: “Idan mai azumi ya manta ya ci ya sha, to ya cika azuminsa domin Allah ne ya ciyar da shi ya shayar da shi.”
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Yin asiwaki da danyen itace ko busasshe ga mai azumi. An karbo daga Amir dan Rabi’ata ya ce: “Na ga Annabi (SAW) yana goge baki da asiwaki yana azumi wanda ba zan iya lisaftawa ba ko kirgawa.” Abu Huraira ya ce daga Annabi (SAW) ya ce: “Ba domin kada in tsananta wa al’ummta ba, da na umarce su da yin asiwaki a kowace alwala.” An ruwaito misalinsa daga Jabir da Zaid dan Khalid daga Annabi (SAW) ya ce: “Tsarki ne ga baki, kuma neman yardar Ubangiji ne.” Adda’u da kattada suka ce, “Babu laifin hadiye tuka (abin asiwaki)”:
394. An karbo daga Abdan ya ce: “Ma’amar ya ba mu labari, ya ce, Zuhuri ya ba ni labari daga Adda’u dan Yazid daga Humran ya ce, “Na ga Usman (Allah Ya yarda da shi) ya yi alwala, ya zuba ruwa a hannunsa ya wanke sau uku. Sa’an nan ya kurkure baki, ya shaka ruwa sa’an nan ya wanke fuskarsa sau uku. Sa’an nan ya wanke hannunsa na dama zuwa gwiwar hannu sau uku. Sa’an nan ya wanke hannunsa na hagun zuwa gwiwar hannu sau uku. Sa’an ya shafa kansa, sa’an nan ya wanke kafarsa ta dama sau uku, ya wanke kafarsa ta hagun sau uku. Sa’an nan ya ce: “Na ga Manzon Allah (SAW) ya yi alwala kamar alwalata wannan, sa’an nan ya ce: “Wanda ya yi alwala kamar alwalata wannan, kuma ya yi Sallah raka’a biyu bai yi hira cikin ransa da wani abu ba face an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa.”
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS:
Da maganar Annabi (SAW) cewa: “Idan mutum zai yi alwala to lallai ya shaka ruwa a hancinsa.” Bai bambanta tsakanin mai azumi da mara azumi ba. Alhassan ya ce, “Babu laifi mai azumi ya yi amfani da sansane (shaka kamar abu mai kanshi), idan ba zai shiga makoshinsa ba, kuma mai azumi yana iya sanya kwalli (tozali). Adda’u ya ce, “Babu laifi ga mai azumi ya kurkure bakinsa ya zubar sai ya hadiye abin da ke bakinsa na miyu. Mai azumi ba ya cin danko, amma idan ya ci ya hadiye miyau na danko ban ce azuminsa ya karye, amma dai an hana shi game da haka. Idan mai azumi ya shaka ruwa sai ruwan ya shiga makoshinsa (makogoro) babu laifi idan bai iya dawowa da shi.”