Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 01
Babi na Sittin da Biyu: Azumi daga karshen wata: 443. An karbo daga Saltu dan Muhammad ya ce: “Mahdiyyu ya ba mu labari daga Ghailan Hawwala Sanad ya ce, Abu Nu’aman ya ba mu labari ya ce, Mahdiyyu dan Maimun ya ba mu labari, ya ce, Ghailan dan Jarir ya ba mu labari daga Mudarrif […]
Babi na Sittin da Biyu: Azumi daga karshen wata:
443. An karbo daga Saltu dan Muhammad ya ce: “Mahdiyyu ya ba mu labari daga Ghailan Hawwala Sanad ya ce, Abu Nu’aman ya ba mu labari ya ce, Mahdiyyu dan Maimun ya ba mu labari, ya ce, Ghailan dan Jarir ya ba mu labari daga Mudarrif daga Imran dan Husain (RA) daga Annabi (SAW) cewa: “Lallai shi an tambaye shi, ko ya ce, ya tambayi wani mutum lokacin Imran yana ji, ya ce: “Ya Baban wane! Shin ka yi azumin karshen wannan wata? Ya ce, “ina tsammaninsa, ya ce, “yana nufin watan Ramadan.” Sai mutumin ya ce, “A’a, ya Manzon Allah! Ya ce, “Idan ka kare Azumin Ramadan (shan ruwa), to ka yi azumin kwana biyu (cikin Shawwal).” Amma Saltu bai ambaci cewa, yana nufin watan Ramadan ba.” Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, “Sabit ya ce daga Mudarrif daga Imran daga Annabi (SAW) amma ya ambaci cewa; “Shin ba ka yi azumin karshen watan Sha’aban (ba)?”
Babi na Sittin da Uku: Azumin ranar Juma’a. Idan mutum ya wayigari da niyyar azumi ranar Juma’a dole ya karya azumin (idan bai yi azumi ranar alhamis ba, ko kuma bai yi niyyar azumin yinin Asabar ba):
444. An karbo daga Abu Asim ya ce, “Daga dan Juraij daga Abdulhamid dan Jubair dan Shaiba daga Muhammad dan Abbad ya ce, ‘Na tambayi Jabir (RA) cewa: “Shin Annabi (SAW) ya hana game da azumin ranar Juma’a ne? Ya ce, “Na’am,” wasu sun kara da cewa, “(Annabi) ya hana kebance ranar da yin azuminta.”
445. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, “A’amashi ya ba mu labari ya ce, Abu Salih ya ba mu labari daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Kada dayanku ya yi azumin ranar Juma’a face ya yi azumin yinin gabaninta ko zai yi a bayanta.”
446. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Shu’abah -Hawwala Sanad- ya ce, “Muhammad ya ba ni labari ya ce, Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga kattada daga Abu Ayyub daga Juwairiyya ’yar Haris (RA), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya shiga gare ta a ranar Juma’a lokacin tana azumi, sai ya ce, “Shin kin yi azumi jiya? Ta ce, “A’a,” ya ce, “To kina son gobe ki yi azumin? Ta ce, “A’a,” ya ce, “To ki karya.” Hammad dan Ja’ad ya ce, ya ji kattada ya ce, Abu Ayub ya ba ni labari cewa: “Lallai Juwairiyya ta ba shi labari cewa: “Sai (Annabi) ya umurce ta da karyawa.”
Babi na Sittin da Hudu: Shin mutum zai iya kebance wani yini da ibada:
447. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba ni labari daga Sufiyan daga Mansur daga Ibrahim daga Alkamata cewa: Na cewa A’isha (RA), cewa: “Shin Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kebance wani yini da wani aikin ibada? Ta ce, “A’a, aikinsa ya kasance madawwami, kuma wane ne cikinku ke iya abin da Manzon Allah (SAW) ya kasance yana iyawa?”