Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 04

Babi na Hudu: Ana neman Daren Lailatul kadari a goma na karshen Ramadan da haka Ubbadu ya ba da labari daga Annabi (SAW): 473. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce, “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari ya ce, Abu Suhail ya ba mu labari daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 04
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 04

Babi na Hudu: Ana neman Daren Lailatul kadari a goma na karshen Ramadan da haka Ubbadu ya ba da labari daga Annabi (SAW):

473. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce, “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari ya ce, Abu Suhail ya ba mu labari daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku nemi Daren Lailatul kadari a cikin wutirin (mara) na goman karshen Ramadan.”

474. An karbo daga Ibrahim dan Hamza ya ce, “dan Abu Hazim Darawardi ya ba mu labari daga Yazid daga Muhammad dan Ibrahim daga Abu Salmata daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana makwabtar (masallaci da I’itikafi) a cikin Ramadan a kwanaki goma na tsakiyar wata. Idan ya kasance lokacin yinin dare na Ashirin ya zo ya shude daren Ashirin da daya ya fara sai ya koma gidansa. Wadanda suke tare da shi a I’itikafin sai su koma tare da shi, kuma lallai shi yakan tsaya ya yi wa mutane huduba a watan da ke I’itikafi kuma a daren da ya kasance zai koma cikinsa, yakan umarce su da abinda Allah Ya so, sa’an nan ya ce: “Na kasance ina I’itikafin wannan wata, kuma lallai ya bayyana mini cewa, lallai zan yi I’itikafin goma na karshen wannan wata bana. Wanda ya kasance ya yi I’itikafi tare da ni to ya zauna a wuirin I’itikafinsa domin an nuna mini Daren Lailatul kadari acikin wannan dare amma an mantar da ni, don haka ku neme shi a cikin goma na karshen, kuma ku rika nemansa a cikin wurin (mara, 21 da  23 da 25 da 27 da 29). Kuma lallai na gan ni a wannan lokaci ina sujuda a cikin ruwa da tabo. Sai sama ta yi kuka (motsin hadari) a wannan dare, sama ta yi ruwa masallaci ya yi zuba a wurin Sallar Annabi (SAW) a dare na Ashirin da daya (21). Kuma lallai fuskar Manzon Allah (SAW) ta bayyana gare ni, na gan shi lokacin da ya juya daga Sallar Asuba fuskarsa tana cike da tabo da ruwa.”
475. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Hisham ya ce, Babana ya ba ni labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), daga Annabi (SAW) ya ce, “Ku neme Daren Lailatul kadari a goma na karshen Ramadan.”
476. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdatu ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a goma na karshen Ramadan yana cewa: “Ku nemi Daren Lailatul kadari a goma na karshen Ramadan.”
477. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Ayyuba ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Hakika Annabi (SAW) ya ce, “Ku nemi Daren Lailatul kadari a cikin goma na karshen Ramadan, a cikin tara na karshe (29), ko cikin bakwai na karshe (27), ko a cikin biyar na karshe (25).”
478. An karbo daga Abdulwahid dan Abul Aswad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Asim ya ba mu labari daga Abu Mijliz da Ikramata ya ce: “dan Abbas (Allah Ya yarda da su) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Shi Daren Lailatul kadari yana goma na karshe, kodai a tara da ta shude, ko a bakwai na karshe.” Abdulwahab ya biye masa daga Ayyub daga Khalid daga Ikramata daga dan Abbas cewa: “Ku neme shi a Ashirin da Hudu ga wata.”