Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 05

Babi na Biyar: dauke sanin lokacin Daren Lailatul kadari saboda husumar (fadar) mutane:479. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Khalid dan Haris ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari ya ce, Anas ya ba mu labari daga Ubbadata dan Samit ya ce, “Wata rana Annabi (SAW) ya fto domin […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 05
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 05

Babi na Biyar: dauke sanin lokacin Daren Lailatul kadari saboda husumar (fadar) mutane:
479. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Khalid dan Haris ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari ya ce, Anas ya ba mu labari daga Ubbadata dan Samit ya ce, “Wata rana Annabi (SAW) ya fto domin ya ba mu labari game da lokacin ganin Daren Lailatil kadari, sai wasu mutane biyu daga cikin Musulmi suna fada. Sai (Annabi) ya ce, “Na fito domin in ba ku labari game da Lailatul kadari sai wane da wane suna fada sai aka dauke (mantar da ni), ina fatar ya kasance alheri gare ku. Ku neme shi a cikin (ashirin da) tara ko bakwai ko biyar.”
 Babi na Shida: Ayyukan alheri a goma na karshen Ramadan:
480. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “dan Uyainata ya ba mu labari daga Abu Ya’afur daga Abu Duha daga Masruk daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance idan goma na karshen Ramadan ya shigo sai ya tattara (daura) gyautonsa ya raya daren kuma yana farkar da iyalansa.”

Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.

Babi kan I’itikafi:

Babi na Farko:
Yin I’itikafi a goma na karshen Ramadan da bayanin hukuncin yin I’itikafi a kowane masallaci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku rungume su alhali kuna masu I’itikafi a cikin masallatai, wadannan iyakokin Allah ne kada ku kusance su. Kamar haka Allah ke bayyana muku ayoyinSa tsammaninku ku yi takawa.” (k:2:187):

481. An karbo daga Isma’ilu dan Abdullahi ya ce: “dan Wahab ya ba mu labari daga Yunus cewa: “Lallai Nafi’u ya ba shi labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a goma na karshen Ramadan.”

482. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab daga Urwata dan Zubair daga A’isha matar Annabi (SAW – Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya kasance yana I’itikafi a goma na karshen Ramadan har Allah Ya karbi ransa. Sa’an nan matansa sun yi I’itikafi a bayansa.”
483. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Yazid dan Abdullahi dan Had ya ce daga Muhammad dan Ibrahim dan Haris Taimiyu daga Abu Salmata dan Abdurrahman daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a goma ga wata na tsakiyar Ramadan. Wata shekara ya yi I’itikafi har sai da daren Ashirin da daya ya kasance shi ne daren da ke fita cikinsa da safe a I’itikafinsa zuwa ga iyalansa. Sai ya ce, “Wanda ya kasance ya yi I’itikafi tare da ni, to lallai ya zarce da I’itikafinsa har zuwa goma na karshe. Hakika an nuna mini Daren Lailatul kadari a wannan dare, sa’an nan an mantar da ni, kuma lallai na gan ni ina sujuda a cikin ruwa da tabo a washegarinsa. Ku neme shi a cikin goma na karshe, kuma ku neme shi a kowane mara (wutiri). Sai sama ta yi ruwa a wancan dare, kuma Masallaci ya kasance bisa rufin itacen dabino don haka masallacin ya yi zuban ruwa. Sai idanuwana suka ga alamar ruwa da tabo a fuskar Manzon Allah (SAW) a washegarin Ashirin da daya ga wata.”