Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 07
Babi na Takwas: Shin mai I’itikafi zai iya fita zuwa kofar masallaci idan da wata bukata?: 490. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husain (Allah Ya yarda da su), ya ba mu labari cewa: “Lallai Safiya matar Annabi (SAW) ta ba shi labari […]
Babi na Takwas: Shin mai I’itikafi zai iya fita zuwa kofar masallaci idan da wata bukata?:
490. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husain (Allah Ya yarda da su), ya ba mu labari cewa: “Lallai Safiya matar Annabi (SAW) ta ba shi labari cewa, lallai ita ta je ga Manzon Allah (SAW) domin ziyararsa a cikin I’itikafinsa a Masallaci kuma a goma na karshen Ramadan, ta yi hira a wurinsa na sa’a daya, sa’an nan ta mike za ta koma. Sai Annabi (SAW) ya mike tare da ita domin ya raka ta har sai da ta kai kofar Masallaci kusa da kofar Ummi Salma sai wasu mutum biyu daga mutanen Madina suka zo wucewa, suka yi wa Manzon Allah (SAW) sallama, sai Annabi (SAW) ya ce, musu ku tafi da natsuwa ina tare da matata ce, Safiyya ’yar Huyayyi sai suka ce, “Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga Allah! Ya Manzon Allah, haka ya yi musu girma.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Hakika Shaidan yana isar wa (mutum da mugun zato a cikin jiki) har inda jini ke isarwa. Kuma lallai ni, na ji muku tsoron kada (Shaidan) ya jefa wani abu a cikin zuciyarku.”
Babi na Tara: I’itikafi da bayanin fitar Annabi (SAW) a safiyar ashirin da daya ga watan Ramadan:
491. An karbo daga Abdullahi dan Munir ya ce: “Ya ji Haruna dan Isma’il ya ce, Aliyu dan Mubarak ya ce, Yahya dan Abu Kasir ya ba ni labari ya ce, “Na ji Abu Salma dan Abdurrahman ya ce, “Na tambayi Abu Sa’idul Khudri na ce, “Shin ko ka ji Manzon Allah (SAW) yana ba da labarin Lailatul kadari? Ya ce, “Na’am, mun yi I’itikafi tare da Manzon Allah (SAW) a goma na tsakiyar watan Ramadan, ya ce: “Mun kasance mukan fita a safiyar ashirin da daya, ya ce, Manzon Allah (SAW) ya yi mana huduba a safiyar ashirin ga wata ya ce: “An nuna mini Daren Lailatul kadari kuma lallai ni, an mantar da ni. Ku neme shi a goma na karshe kuma a cikin wutiri (mara). Kuma lallai na gan ni ina sujuda a cikin ruwa da tabo. Wanda ya kasance na I’itikafi tare da Manzon Allah (SAW), to ya komo (har zuwa karshen wata). Sai mutane suka komo zuwa Masallaci, ba mu ga komai ba a sama na hadari, ya ce, “Sai wani gigije ya zo ya yi ruwa aka tsayar da Sallah Manzon Allah (SAW) ya yi sujuda a cikin tabo da ruwa, kuma har sai da na ga tabo bisa hancinsa da goshinsa (SAW).”
Babi na Goma: I’itikafin mai Istihala (jinin da ba haila ba):
492. An karbo daga kutaiba ya ce: “Yazid dan Zurai’u ya ba mu labari daga Khalid daga Ikramata daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce; “Wata mace mai Istihala daga matansa (Annabi) ta yi I’itikafi tare da Manzon Allah (SAW), har ta kasance tana ganin jini ja-ja da launin rawaya. Da yawa mukan sanya tasa (daro) a karkashinta lokacin da take Sallah.”