Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 08
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.Littafin Bayanin Sallar Tarawihi (Asham): Babi na Farko: Fifikon wanda ya yi tsayuwar Ramadan da kyawun ayyuka: 465. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab ya ce, Abu Salmata ya ba ni labari cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah […]
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.
Littafin Bayanin Sallar Tarawihi (Asham):
Babi na Farko: Fifikon wanda ya yi tsayuwar Ramadan da kyawun ayyuka:
465. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukailu daga dan Shihab ya ce, Abu Salmata ya ba ni labari cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, game da Ramadan: “Wanda ya tsayu da shi da imani kuma domin neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunbabansa.”
466. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Humaid dan Abdurrahman daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya tsayu a cikin Ramadan da imani domin neman lada an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubbansa.” dan Shihab ya ce, “An karbi ran Manzon Allah (SAW) mutane na kan haka. Sa’an nan al’amari ya kasance a hannun halifancin Abubakar har lokacin rabin halifancin Umar (Allah Ya yarda da su).” An karbo daga dan Shihab daga Urwata dan Zubair daga Abdurrahman dan Abdul kari’u cewa, lallai shi ya ce: “Na fita tare da Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi) a wani daren Ramadan zuwa masallaci, sai muka iske mutane kungiya daban-daban, wani na wa kansa Sallah, wani kuma na yi wa wasu jama’a limanci. Sai Umar ya ce, “Lallai ina ganin da dai na tara wadannan bisa ga wani masanin Alkur’ani ya fi zama abin koyi. Sa’an nan ya shirya ya tara su bisa ga limancin Ubayyu dan Ka’ab. Sa’an nan na fito tare da shi a wani daren sai muka iske mutane suna Sallah da limaminsu masanin Alkur’ani.” Umar ya ce, “Madalla da wannan kirkira (tsari), wanda suke barci ga barinta (zuwa karshen dare) sun fi masu tsayuwa da ita, yana nufin karshen dare. Sai mutane suka rika tsayuwa da ita Sallar a farkon dare.”
467. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga dan Shihab daga Urwata dan Zubair daga A’isha matar Annabi (SAW) -Allah Ya yarda da ita- cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana Sallar a dararen Ramadan.”
468. An karbo daga Yahya da nBukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab ya ce, Urwata ya ba ni labari cewa: “Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba shi labari cewa; “Hakika Manzon Allah (SAW) ya fita a cikin wani dare mai duhu ya yi Sallah a masallaci, wasu jama’a suka yi koyi da sallarsa. Sai mutane suka wayi gari suna hira (labari) game da haka, sai wadanda suka fi su yawa suka taru washe gari suka yi Sallah tare da shi. Mutane suka wayi gari suna hira game da haka, mutanen masallaci suka taru da yawa a dare na uku, Manzon Allah (SAW) ya fita suka yi koyi da sallarsa. A dare na hudu sai da masallaci ya gaza wa jama’a, (Annabi) bai fita ba har sai da gari ya waye ga Sallar Safiya lokacin da ya kare Sallar Safe, sai ya fuskanci mutane ya yi tashahhudi (kalmar shahada domin fara jawabi). Sa’an nan ya ce, “Bayan haka, amma taruwanku jiya bai buya gare ni ba. Amma lallai ni, ina ji muku tsroron kada a farlanta muku yin Sallar, sai ku gajiya ga barinta.” A nan haka Manzon Allah (SAW) ya rasu al’amari bai canja ba a kan haka.”