Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 09

  469. An karbo daga Isma’ilu ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Sa’idul Makburi daga Abu Salmata dan Abdurrahman cewa: “Lallai shi ya tambayi A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Yaya Sallar nafilar Manzon Allah (SAW) ta kasance a cikin Ramadan?” Ta ce, “Bai kasance yana kara komai ba cikin Ramadan ko […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 09
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 09

 

469. An karbo daga Isma’ilu ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Sa’idul Makburi daga Abu Salmata dan Abdurrahman cewa: “Lallai shi ya tambayi A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Yaya Sallar nafilar Manzon Allah (SAW) ta kasance a cikin Ramadan?” Ta ce, “Bai kasance yana kara komai ba cikin Ramadan ko waninsa fiye da raka’a goma sha daya. Yana Sallah raka’a hudu kada ka tambaya game da kyawonsu da tsawonsu (ma’ana dai suna da kyau kwarai). Sa’an nan ya yi Sallah raka’a hudu kada ka tambaya game da kyawonsu da tsawonsu. Sa’an nan yana yin Sallah raka’a uku (sun zama goma sha daya ke nan). Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Shin kana barci ne kafin ka yi wutiri? Ya ce, “Ya A’isha! Hakika idanuwana suna barci amma zuciyata ba ta barci.”

Babi na Biyu: Fifikon Daren Lailatul kadari. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne Mu, Muka saukar da shi a Daren Daraja. Me ya sanar da kai Daren Daraja…..(har zuwa karshen Surar.”(k:97: 1-2).  dan Uyainata ya ce: “Duk abin da Alkur’ani ya ce: “Me ya sanar da kai, to lallai zai sanar da mutum shi wannan abu.” Amma idan Alkur’ani ya ce, “Shin ka san,” to babu wanda ya san shi.”:

470. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, mun kiyaye shi, amma ya haddace shi daga Zuhuri ne cewa: Daga Abu Salmata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wanda ya azumci Ramadan da imani kuma domin neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubbansa. Wanda ya tsayu da aikin kwarai a daren Ramadan da imani kuma domin neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubbansa.” Sulaiman dan Kasir ya biye masa daga Zuhuri.

Babi na Uku:  Neman Daren Lailatul kadari a cikin kwanaki bakwai na karshen Ramadan:

471. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai wasu mutane daga sahabban Annabi (SAW) an nuna musu Daren Lailatul kadari a cikin mafarki a kwanaki bakwai na karshen Ramadan. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ina ganin mafarkinku ya dace da kwanaki bakwai na karshen Ramadan. Duk wanda zai neme shi, to, ya neme shi a cikin bakwai din karshe.”

472. An karbo daga Mu’azu dan Faddala ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Yahya daga Abu Salmata ya ce, “Na tambayi Abu Sa’id ya kasance aboki gare ni. Ya ce, “Mun yi I’itikafi tare da Annabi (SAW) a Goma na tsakiyar Ramadan. Sai ya fito a safiyar yini na Ashirin ya yi mana huduba ya ce, “Lallai ni, an nuna mini Daren Lailatul kadari, sa’an nan aka mantar da ni to ku neme shi a cikin Goma na karshen Ramadan kuma a mara (wutiri). Kuma lallai na gan ni a wannan lokacin ina sujuda a cikin ruwa da tabo wanda duk yake I’itikafi tare da ni, to ya komo mu ci gaba (a Goman karshe). Sai muka komo ba mu ga wani duhun girgije a cikin sama ba, sai muka giragizai sun zo suka saukar da ruwa har sai da rufin Masallaci ya yi yoyo (zuba) saboda rufinsa ya kasance daga tankar dabino. Aka tsayar da Sallah na ga Manzon Allah (SAW) yana sujuda a cikin ruwa da tabo, har sai da naga alamar tabon a goshinsa (fuska).”