Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 1
403. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Hamza dan Amrul Aslami ya ce da Annabi (SAW) shin zan iya azumi a cikin tafiya? Ya kasance mai yawan azumi, sai (Annabi) […]
403. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha matar Annabi (SAW) (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Hamza dan Amrul Aslami ya ce da Annabi (SAW) shin zan iya azumi a cikin tafiya? Ya kasance mai yawan azumi, sai (Annabi) ya ce, “Idan ka so ka yi azumi, idan ka so kuma ka ci.”
Babi na Talatin da Hudu: Idan mutum ya fara azumi daga Ramadan sa’an nan ya fara tafiya:
404. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbah daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa Makka a cikin Ramadan sai ya yi azumi. Lokacin da ya isa Kadid sai ya ci abinci mutane sai suka ci.” Abu Abdullahi ya ce, “Kadid wani ruwa ne a tsakanin Usfan da kudaid.”
Babi na Talatin da Biyar: Kamar abin da ya gabata:
405. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Yahya dan Hamza ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Yazid dan Jabir cewa: “Isma’il dan Ubaidullahi ya ba shi labari daga Ummu Darda’i daga Abu Darad’i (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun fita tare da Manzon Allah (SAW) a cikin wasu tafiye-tafiyensa a cikin yini mai zafi har mutum yakan sanya hannu a kai saboda tsananin zafi, babu mai azumi cikinmu face Annabi (SAW) da dan Rawah.”
Babi na Talatin da Shida: Da maganar Annabi (SAW) ga wanda aka yi masa inuwa saboda tsananin zafi cewa: “Ba da’a ba ne azumi a cikin tafiya:
406. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Abdurrahman mutumin Madina ya ce: “Na ji Muhammad dan Amru dan Alhasan dan Aliyu daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance a cikin wata tafiya sai ya ga taron jama’a bisa ga wani mutum an yi masa inuwa a kansa sai ya ce, “Mene ne wannan? Sai suka ce, “Mai azumi ne,” sai ya ce, “Ba da’a ba ce, yin azumi a cikin tafiya.”
Babi na Talatin da Bakwai: Sashin Sahabban Annabi (SAW) ba su aibata sashi saboda cin abinci ko yin azumi a tafiya:
407. An karbo daga Abdullahi dan Maslamat ya ce: “Daga Malik daga Humaid dawili daga Anas dan Malik ya ce: “Mun kasance muna tafiya tare da Annabi (SAW) mai azumi ba ya aibata wanda yake cin abinci. Mai cin abinci ba ya aibata mai yin azumi.”
Babi na Talatin da Takwas: Wanda ya ci abinci a cikin tafiya don ya nuna wa mutane:
408. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awanah ya ba mu labari daga Mansur daga Mujahid daga dawus daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya fita daga Madina zuwa Makka alhali ya dauki azumi har sai da ya isa Usfan. Sai ya yi kira da a kawo ruwa ya daukaka shi zuwa hannunsa domin mutane su gan shi, sai ya karya azumi har ya isa Makka, wannan kuma ya faru ne a cikin azumin Ramadan.” dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya kasance yana cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya yi azumi kuma ya sha, saboda haka wanda ya so ya yi azumi, wanda ya so ya ci abinci.”