Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 10
Littafi na Hudu (4) Littafin Kasuwanci Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah Ya halatta saya da sayarwa, amma Ya haramta riba.” (k:2:275) da fadarSa cewa: “Face sai idan ta kasance bisa fatauci halattacce, wanda kuke juya shi a tsakaninku.” (k:2:282). Babi na Farko: Da fadar Allah Madaukaki cewa: […]
Littafi na Hudu (4)
Littafin Kasuwanci
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai
Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah Ya halatta saya da sayarwa, amma Ya haramta riba.” (k:2:275) da fadarSa cewa: “Face sai idan ta kasance bisa fatauci halattacce, wanda kuke juya shi a tsakaninku.” (k:2:282).
Babi na Farko:
Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan aka kare game da tsayar da Sallar (Juma’a), ku watsu a cikin kasa kuma ku nema daga falalar Allah ….” (k:62:10) da fadarSa cewa: “Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da barna face idan ta kasance fatauci bisa yarjejeniya daga gare ku.” (k:4:26).
502. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: “Abul Yaman ya ba mu labari ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce Sa’id dan Musayyab ya ba mu labari da Abu Salmata dan Abdurrahman cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lallai ku, kuna cewa lallai Abu Huraira ya yawaita Hadisi daga Manzon Allah (SAW), kuna cewa, me ya sa Muhajirai da mutanen Madina ba su yawaita Hadisai daga Manzon Allah (SAW) da misalin Hadisin Abu Huraira ba? Amma hakika ’yan uwana Muhajirai tafiya fatauci (kasuwanci) a kasuwanni ya shagaltar da su, na kasance ina lazimtar Manzon Allah (SAW) da abin da ya cika mini ciki kadai. Sai in halarta lokacin da ba su nan, in kiyaye abin da suka manta. ’Yan uwana mutanen Madina aiki bisa dukiyoyinsu ya shagaltar da su, kuma ni na kasance mutum ne miskini daga miskinan As’habu Suffah (mutanen da suke kebe a cikin masallaci) ina tuna abubuwan da suka mance. Kuma lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, a cikin Hadisinsa da ya ba da labari da shi cewa: Babu wanda zai shimfida tufafinsa har na kare magana ta wannan, sa’an nan ya tara tufafin zuwa gare shi face ya haddace abin da nake fadi. Sai na shimfida tufafina (taguwata) har sai da Manzon Allah (SAW) ya kare maganarsa sai na tara ta zuwa ga kirjina, ban mance komai daga maganar Manzon Allah (SAW) tun daga wancan abu (shimfidar taguwa).”
503. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari daga babansa daga kakansa ya ce, “Abdurrahman dan Auf (Allah Ya yarda da shi), lokacin da muka isa Madina Manzon Allah (SAW) ya hada ’yan uwantaka a tsakanina da Sa’ad dan Rabi’ah, sai Sa’ad dan Rabi’ah ya ce, “Lallai ni ne mafi dukiyar mutanen Madina, kuma zan raba dukiyata biyu in ba ka rabi, kuma ka duba daga cikin matana, wadda kake so, sai in sake ta ka aure ta.” Ya ce, “Sai Abdurrahman ya ce, “Ba ni da bukata bisa ga haka, shin akwai kasuwa, wadda ake kasuwanci (fatauci)”? Ya ce, “Eh, akwai Kasuwar kainuka’u,” sai ya ce, “Sai Abdurrahman ya tafi ya zo da cuku da mai,” sa’an nan ya rika fita kullum. Ba a dade ba, sai ga Abdurrahman ya zo da alamar kunshi na aure, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka yi aure ne?” Ya ce, “Na’am.” Ya ce, “Da wacce?” Ya ce, “Da wata mace daga matan Madina.” Ya ce, “Nawa ka biya sadaki?” Ya ce, “Nauyin dan dabino na zinari,” sai Annabi (SAW) ya ce, “To, ka yi walima ko da da akuya (tunkiya) ce.”