Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 11
Babi na Goma: Fita zuwa fatauci (kasuwanci) bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku watsu a cikin kasa ku nema daga kyautar Allah (kasuwanci)” (k:62:10). 516. An karbo daga Muhammad ya ce: “Makhlad danYazid ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Adda’u ya ba ni labari daga Ubaidu dan […]
Babi na Goma:
Fita zuwa fatauci (kasuwanci) bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku watsu a cikin kasa ku nema daga kyautar Allah (kasuwanci)” (k:62:10).
516. An karbo daga Muhammad ya ce: “Makhlad danYazid ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Adda’u ya ba ni labari daga Ubaidu dan Umair cewa: Lallai Abu Musa ya nemi izinin Umar (Allah Ya yarda da shi), amma bai yi masa izini ba. Kamar ka ce shi ya kasance wanda aka shagaltar, sai Abu Musa ya koma lokacin da Umar ya samu sarari sai ya ce, “Ban ji muryar Abdullahi dan kaisu ba? Ku yi masa izini.” Sai aka ce, “Hakika ya koma.” Sai ya kira shi, (Abu Musa) ya ce, “Mun kasance ana umurtaermu da haka (komawa idan ba a yi mana izini ba).” Ka tafi zuwa ga mazaunar mutanen Madina, ka samo mini hujja a kan haka daga wani. Sai ya tafi gidajen mutanen Madina ya tambaye su game da haka suka ce, “Babu wanda zai ba ka shaidar wannan face yaron da ke cikinmu shi ne Abu Sa’idul Khudri, sai ya tafi da Abu Sa’idul Khudri sai Umar ya ce, “Yanzu wannan ya fini sanin al’amarin da ya buya mini daga Manzon Allah (SAW)? Fataucina da kasuwanni ya shagaltar da ni, yana nufin fita zuwa kasuwanci.”
Babi na Goma Sha daya:
Yin fatauci a bisa kogi, Madaru ya ce, “Babu laifi game da haka,” bisa abin da Allah Ya ambace shi a cikin Alkur’ani da gaskiya cewa: “Za ka ga jirage masu ketawa cikinsa domin ku nema daga kyautarsa (kasuwanci)” (k:16:14). Ma’anar fulku sufunu jiragen ruwa, sufun jam’in e kuma haka yake ga sunan daya. Mujahid ya ce, “Jirage suna ketawar iska amma iska ba ta keta komai daga jiragen ruwa face jirage manya. Laisu ya ce, “Ja’afar dan Rabi’ata ya ba ni labari daga Abdurrahman dan Hurmuz daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon Allah (SAW) cewa, lallai shi ya ambaci wani mutum daga Bani Isra’il da ya fita bisa kogi ya biya bukatarsa sai ya kora Hadisin, ya ce, “Abdullahi dan Salih ya ba ni labari ya ce, “Laisu ya ba mu labari.”
Babi na Goma Sha daya:
Da maganar Allah Madaukaki cewa: “Idan sun ga abin fatauci ko wani abin shagala sai su watse zuwa gare su…” (k:62:11). Da fadarSa cewa: “Fatauci da kasuwanci ba ya shagaltar da su game da ambaton Allah…” (k:24:37). kattada ya ce: “Mutane sun kasance suna fatauci da kasuwanci idan wasu hakkokin Allah sun gabata musu sai su gabatar da hakkin Allah a kan fatauci da kasuwanci bai shagaltar da su game da ambato Allah ba face sun bayar da shi (hakkin) zuwa ga Allah.”
517. An karbo daga Muhammad ya ce: “Muhammad dan Fudail ya ba mu labari daga Husain daga Salim dan Abu Ja’ad daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Wasu ayarin ’yan kasuwa sun iso daga Siriya lokacin muna Sallah tare da Annabi (SAW) a ranar Juma’a, sai mutane suka watse face mutum goma sha biyu, sai wannan aya ta sauka cewa: “Idan suka ga kayan fatauci ko abin shagala sai su watse zuwa gare su, su barka a tsaye…” (k:62:1).