Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 12

Babi na Goma Sha Biyu: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku ciyar daga abubuwa tsarkaka daga abin da kuke tsiwirwitawa (samu)..” (k:2:267). 518. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Abu Wa’il daga Masruk daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 12
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 12

Babi na Goma Sha Biyu:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku ciyar daga abubuwa tsarkaka daga abin da kuke tsiwirwitawa (samu)..” (k:2:267).

518. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Abu Wa’il daga Masruk daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Idan mace ta ciyar da abinci daga dakinta ba tare da barna ba, tana da ladarta bisa ga abin da ta ciyar, mijinta kuma na da ladar nemowa, mai tsaron taska ma na da ladar misalin haka (idan ya ciyar) sashinsu ba ya tauye komai daga ladar sashi.”

519. An karbo daga Yahya dan Ja’afar ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam ya ce, “Na ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce, “Idan mace ta ciyar daga kayan (abincin) mijinta ba tare da umarninsa ba tana da rabin ladarsa.”

Babi na Goma Sha Uku: Wanda ke son a kara shimfida masa arziki:

520. An karbo daga Muhammad dan Abu Yakub Alkurmani ya ce: “Hassan ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari ya ce, Muhammad Zuhuri ya ce, daga Anas dan Malik ya ba mu labari ya ce, “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, “Wanda zai masa farin ciki (dadi) a kara masa arzikinsa ko a kara masa shekaru, to, lallai ya sadar da zumuntarsa.”

Babi na Goma Sha Hudu: Ciniki da ba shi wanda Annabi (SAW) ya aikata:

521. An karbo daga Mu’allah dan Asad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, “Mun ambata game da jingina a cikin ciniki a wurin Ibrahim sai ya ce, “Aswad ya ba ni labari daga Aisha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya sayi abinci daga wani Bayahude zuwa ajali ya yi jinginar wata taguwa (sulke) ta bakin karfe.”

522. An karbo daga Muslim ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba mu labari daga Anas -Hawwala Sanad- ya ce, “Muhammad dan Abdullahi dan Haushab ya ba ni labari ya ce, jikokin Abu Yasa’a mutumin Madina sun ba mu labari, ya ce, “Hisham Distawa’iyu ya ba mu labari daga kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa, “Lallai shi ya tafi zuwa ga Annabi (SAW) da waina ta sha’ir da wani abu na garin abinci. Kuma lallai Annabi (SAW) ya taba jinginar da taguwarsa (sulke) a Madina ga wani Bayahude don ya karbi garin shai’ri ga iyalansa. Kuma lallai na ji shi (Anas) yana cewa: “Wata rana iyalan Annabi Muhammad (SAW) sun yini ba su da ko Sa’i daya na alkama ko na garin abinci alhali lokacin yana da mata tara.”

 Babi na Goma Sha Biyar: Neman abincin mutum bisa ga abin da hannunsa ya aikata:

523. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “dan Wahab ya ba mu labari, daga Anas daga dan Shihab ya ce, “Urwat dan Zubair ya ce, lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lokacin da aka halifantar da Abubakar ya ce, “Hakika mutanena sun sani cewa, lallai sana’ata ba ta isarwa ga bukatun iyalaina, kuma ga shi na shagalta da al’amuran Musulmi, shin iyalan Abubakar za su ci daga wannan dukiyar baitul mali na Musulmi ko zan iya wa Musulmi aiki.”

524. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi dan Yazid ya ba mu labari ya ce, Sa’id ya ba mu labari ya ce, Abul Aswad ya ba ni labari ya ce, “A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce, “Sahabban Manzon Allah (SAW) sun kasance masu ayyuka da kawunansu, har ya kasance suna karni (zufa), sai aka ce musu: Da dai kuna rika wanka.” Hammamu ya ruwaito shi daga Hisham daga Babansa daga A’isha.