Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 13

Babi na Ashirin: Idan masu ciniki biyu suka bayyana komai game da kayan fatauci kuma suka yi nasiha (Allah Zai sanya albarka a cikin kasuwancinsu). An karbo daga Adda’u dan Khalid ya ce, “Annabi (SAW) ya rubuta mini takarda cewa: “Wannan shi ne abin da Muhammad Manzon Allah (SAW) ya saya daga Adda’u dan Khalid […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 13
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 13

Babi na Ashirin:

Idan masu ciniki biyu suka bayyana komai game da kayan fatauci kuma suka yi nasiha (Allah Zai sanya albarka a cikin kasuwancinsu). An karbo daga Adda’u dan Khalid ya ce, “Annabi (SAW) ya rubuta mini takarda cewa: “Wannan shi ne abin da Muhammad Manzon Allah (SAW) ya saya daga Adda’u dan Khalid bisa cinikin mutum Musulmi da Musulmi (bisa ga cinikin wannan bawa) ba mai cuta ba kuma ba mai mummuna hali irinsu sata ba.” kattada ya ce, “Ma’anar Alga’ilatu: Zina da sata da gudu.” An ce wa Ibrahim wasu dillalai sukan rika kiran igarmansu na dawaki cewa, “Ingarman Khurasan ne da Sigtisan, ko suka rika cewa, “Jiya ya zo daga Khurasan, wannan kuma yau ya zo daga Sigtisan.” Sai ya nuna kin sa ga haka kwarai. Ukba dan Amir ya ce, ga wani mutum da zai sayar da kayansa ya san cewa: “Lallai akwai cuta tare da ita, face sai ya sanar da ita.”

532. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce, “Shu’aba ya ba mu labari daga kattada daga Salih Abul Khalil daga Abdullahi dan Haris ya daukaka shi zuwa ga Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Masu ciniki biyu suna da zabi matukar suna tare ba su rabu ba. Ko ya ce, “Har sai sun rabu, idan sun yi gaskiya suka bayyana sai a sanya musu albarka cikin cinikinsu. Idan suka boye aibi suka yi karya sai a cire musu albarkar cinikinsu.”

Babi na Ashirin da daya: Cinikin gaurayayyen dabino:
533. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Shaiban ya ba mu labari daga Yahya daga Abu Salmata daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance ana azurta mu daga dabino gaurayayye (ganima) shi ne gaurayen dabino. Mukan saya rda sa’i biyu da sa’i daya na dabino (mai kyau). Sai Annabi (SAW) ya ce: “Kada ku sayar da sa’i biyu da sa’i daya. Kuma ban da Dirhami biyu bisa ga Dirhami daya.”   

Babi na Ashirin da Biyu: Abin da aka ce game da mai sayar da nama da mahauci:
534. An karbo daga Umar dan Hafsu ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce, “Shakiku ya ba ni labari daga Abu Mas’ud ya ce, “Wani mutum ya zo daga mutanen Madina wanda ake masa alkunya da Abu Shu’aib sai ya ce, wa yaronsa mai sayar da nama. Ka sanya mini abinci (nama) da zai isar (kosar) da mutane biyar domin ina son in gayyaci Annabi (SAW) tare da mutum biyar. Domin lallai ni, na fahimci yunwa a cikin fuskarsa. Sai ya gayyace su (Annabi), wani mutum ya biyo su sai Annabi (SAW) ya ce, “Wannan ya biyo mu, idan ka so ka yi masa izini, idan ka so ya koma sai ya koma, sai (mutumin) ya ce, “A’a, hakika na yi masa izini.”

Babi na Ashirin da Uku: Abin da karya da boye aibi ke jawowa na rashin albarkan ciniki:

535. An karbo daga Badal dan Muhabar ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga kattada ya ce: “Na ji Abul Khalil yana ba da labari daga Abdullahi dan Haris daga Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Masu ciniki biyu suna da zabi matukar suna tare ba su rabu ba. Idan suka yi wa juna gaskiya suka bayyana aibi sai a sanya albarka a cikin cinikinsu. Idan suka boye aibi suka yi wa juna karya, sai a cire albarka a cinikinsu.”