Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 14
Babi na Ashirin da Hudu: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci riba ninkin ba ninki….har karshen aya” (k:3:130). Babi na Ashirin da Biyar: Hukuncin mai cin riba da mai shaida da mai rubutunta. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Wadannan da suke cin riba ba za su tsayu […]
Babi na Ashirin da Hudu:
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci riba ninkin ba ninki….har karshen aya” (k:3:130).
Babi na Ashirin da Biyar:
Hukuncin mai cin riba da mai shaida da mai rubutunta. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Wadannan da suke cin riba ba za su tsayu ba Ranar kiyama face kamar wanda yake fama da tabuwar hankali…” (k:2:275).
536. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari daga Shu’aba daga Mansur daga Abu Duhah daga Masruk daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lokacin da karshen ayoyin suratul Bakara suka sauka sai Annabi (SAW) ya karanta su a kansu (mutane) a Masallaci, sa’an nan ya haramta cinikin giya.”
537. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Jariru dan Hazim ya ce, Abu Raja’u ya ba mu labari, daga Samurata dan Jundab (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Na gani a cikin wani dare da wasu mutane da suka zo mini suka fitar da ni zuwa wata kasa mai tsarki, sai muka tafi har sai da muka je ga wata korama na jini inda wani mutum ke tsaye kuma a gefen (gabar) koramar akwai wani mutum a tsaye da duwatsu cikin hannuwansa. Sai mutumin da ke cikin koramar nan ya fuskanto, ya yi nufin fita sai mutumin mai duwatsu ya jefe shi a cikin bakinsa da duwatsun nan, sai ya mayar da shi inda yake. Sai ya kasance duk lokacin da ya fito sai ya jefe shi a cikin bakinsa da dutse, sai ya koma inda yake. Sai na ce, “Wane ne wannan? Sai (Mala’ika) ya ce, “Wanda ka gan shi a cikin korama (kogi) nan mai cin riba ne.”
Babi na Ashirin da Shida:
Laifin mai ba da riba bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka ba da gaskiya ku ji tsoron Allah ku bar abin da ya saura daga riba in kun kasance masu imani….har zuwa fadarSa… “Alhali su ba a zaluntar da su komai…” (k:2:278-281).” dan Abbas ya ce, “Wannan ce aya ta karshe da ta sauka ga Annabi (SAW).”
538. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Aunu dan Abu Juhaifa ya ce, “Na ga babana ya sayi wani bawa mai yin kaho, (sai ya karya abin yin kahon) na tambaye shi game da haka ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da kudin kare da kudin jini. Kuma ya hana game da mace mai karin gashi da wanda ake mata karin gashi, ya hana ga mai cin riba da mai bayarwa kuma ya la’ani masu yin hoto.”
Babi na Ashirin da Bakwai:
Kan fadar Allah Madaukaki cewa: “Allah Yana cire albarkar riba, kuma Ya sanya albarkar sadakoki. Allah ba Ya son dukkan mai yawan kafirici mai sabo.” (k:2:276).
539. An karbo daga Yahaya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yunus daga dan Shihab ya ce, dan Musayyab ya ce, Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Rantsuwa na jawo mai ciniki ya sayi kaya, amma kuma (rantsuwa) na cire albarkar (cinikin).”