Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 15

Babi na Ashirin da Takwas: Abin da aka hana game da rantsuwa a cikin ciniki: 540. An karbo daga Amru dan Muhammad ya ce: “Hushaim ya ba mu labari ya ce, Awwam ya ba mu labari daga Ibrahim dan Abdurrahman daga Abdullahi dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Hakika wani mutum ya […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 15
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 15

Babi na Ashirin da Takwas: Abin da aka hana game da rantsuwa a cikin ciniki:

540. An karbo daga Amru dan Muhammad ya ce: “Hushaim ya ba mu labari ya ce, Awwam ya ba mu labari daga Ibrahim dan Abdurrahman daga Abdullahi dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Hakika wani mutum ya mike da wani kayan kasuwanci a cikin kasuwa sai ya rantse da Allah cewa, lallai ya ba da (kashe) kaza alhali bai kashe haka ba, domin ya aukar da (cutar da) wani mutum Musulmi wajen ciniki. Sai wannan aya ta sauka da cewa, “Lallai wadanda suke sayen alkawarin Allah da rantsuwoyinsu bisa ’yan tamanni kadan…har zuwa karshe.” (k:3:77).
Babi na Ashirin da Tara:
Abin da aka ambata game da makeran zinari. dawus da dan Abbas (Allah Ya yarda da su), sun ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Ba a cire makiyayarta (Makka),” sai Abbas ya ce, “Sai dai ban da ciyawar tsaure, saboda makeransu da jinkan dakunansu,” (Annabi) ya ce, “To ban da tsaure.”
541. An karbo daga Abdan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari, ya ce, Yunus ya ba mu labari daga dan Shihab ya ce, Aliyu dan Husain ya ba ni labari cewa: “Lallai Husain dan Aliyu (Allah Ya yarda da shi) ya ba shi labari cewa: “Lallai Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na kasance ina da wani tsohon rakumi daga dukiyar ganima kuma Annabi (SAW) ya ba ni wani rabo daga Khumusi (daya cikin biyar na ganima), lokacin da na yi nufin auren Fadima ’yar Manzon Allah (SAW) (Allah Ya yarda da ita), sai na kulla alkawari da wani makeri daga kabilar kainuka’u da ya rika tafiya tare da ni, muna zuwa da ciyawar tsaure, na rika sayarwa ga makera domin in yi amfani da kudin wajen walimar angwancina.”
542. An karbo daga Is’hak ya ce: “Khalid dan Abdullahi ya ba mu labari daga Khalid daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, “Lallai Allah Ya haramta Makka ba ta halatta ga wani gabanina. Kuma ba ta halatta ga wani a bayana. Kuma lallai ni ma an halatta mini ita a wani dan lokaci ne na yini. Ba a cire makiyayarta, kuma ba a cire itacenta, kuma ba a korar abin farautarta, kuma ba a daukar tsintuwarta, face ga mai sanarwa.” Abbas dan Abdul Mudallib ya ce, “Sai dai ban da ciyawar tsaure, saboda makerarmu da rufin dakinmu.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “To, ban da ciyawar tsaure.” Ikramata ya ce, “Shin ko ka san ma’anar korar abin farauta? Shi ne ka kore shi daga inuwa kai ka maye wurinsa ka zauna.” Abdul Wahhab ya ce, daga Khalid cewa: “Saboda makerarmu da kaburburanmu.”
Babi na Talatin: Ambaton makeri da abin da aka ce game da makerin bakin karfe:
543. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “dan Abu Addiyu ya ba mu labari daga Shu’aba daga Sulaiman daga Abu Duha daga Masruk daga Khabbab ya ce: “Na kasance makeri kafin Musulunci, kuma na kasance ina da wani bashi a kan Asi dan Wa’ilu sai na tafi gare shi domin ya biya ni shi. Sai ya ce, “Ban biyanka har sai ka kafirce da Muhammad (SAW).” Na ce, “Ba zan kafirce ba har sai Allah Ya matar da kai, sa’an nan Ya tayar da kai.” Sai (Asi) ya ce, “Bar ni har sai na mutu an tayar da ni, a ba ni ’ya’ya da dukiya sai in biya ka.” Sai wannan aya ta sauka cewa: “Shin ka ga wanda ya kafirce da ayoyinmu, ya ce, “Lallai za a ba ni dukiya da ’ya’ya. Shin ya tsinkayi (san) gaibi ne? A’a, ko ya riki wani alkawri ne da Mai rahama?” (k:19:77-78).