Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 16

Babi na Talatin da daya: Ambaton labarin madinki: 544. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha cewa: “Lallai shi ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Lallai wani madinki ya taba gayyatar Manzon Allah (SAW) saboda wani […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 16
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 16

Babi na Talatin da daya: Ambaton labarin madinki:

544. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha cewa: “Lallai shi ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Lallai wani madinki ya taba gayyatar Manzon Allah (SAW) saboda wani abinci da ya yi ma shi (Annabi).” Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Sai na tafi tare da Manzon Allah (SAW) zuwa ga wancan abincin. Ya kusanto (kawo) wa Manzon Allah (SAW) da waina da miya da aka yi da duma da busasshen nama. Sai na ga Annabi (SAW) yana bin duman nan a gefen akwashi yana ci. (Anas) ya ce, “Ban gushe ba ina son duma (kayan lambu mai kama da kankana na yado) tun daga wannan rana.”

Babi na Talatin da Biyu: Labarin masaki:
545. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Abu Hazim ya ce: “Na ji Sahlu dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wata mace ta zo da wani mayafi wanda aka yi masa dajiyar baki. Ya ce, “Kun san mene Burdat? Sai aka ce masa: “Na’am, wani mayafi ne wanda aka saka (daje) bakinsa. Sai ta ce, “Ya Manzon Allah! “Lallai ni ne, na saka wannan da hannuna domin in kawo maka kyautarsa. Sai Annabi (SAW) ya dauke shi yana kuma mai bukatarsa, ya fito gare mu wata rana yana kamar gyautonsa. Sai wani mutum daga cikin mutane ya ce, “Ya Manzon Allah, ka ba ni kyautarsa,” ya ce, “Na’am, sai Annabi (SAW) ya zauna (shiga) wani mazauni sa’annan ya komo ya nade shi, sa’annan ya aikata gare shi (mutumin). Sai mutane suka ce, masa: “Ba ka kyauta game da rokonsa shi ba (wannan tufafi), lallai ka san cewa, hakika shi (Annabi) ba ya hana mai roko.” Sai mutumin ya ce, “Wallahi ban roke shi domin in daura shi ba, face domin ya kasance mini likkafani a ranar da zan mutu.” Sahlu ya ce, “Sai ya kasance likkafaninsa.”

Babi na Talatin da Uku: Labarin masassaki:
546. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Abdul’aziz ya ba mu labari daga Abu Hazim ya ce, “Wasu mutane sun zo ga Sahlu dan Sa’ad domin tambayarsa game da mumbarin (Annabi). Sai ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya aika zuwa ga wance, (wata mace) Sahlu ya ambaci sunanta, cewa: “Ki umurci yaronki masassaki ya sassaka mini matakala (mumbari) wanda zan rika zama a kansu idan zan yi wa mutane magana (huduba). Sai ta umurce shi da aika ta (sassaka) ta daga goribar daji (gwangwala). Sa’an nan ya zo da ita, ta aika da shi zuwa ga Manzon Allah (SAW) ya umurta aka sanya ta ya zauna bisanta (kanta).”
547. An karbo daga Khallad dan Yahya ya ce: “Abdulwahid dan Aiman ya ba mu labari daga Babansa daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai wata mace daga matan Madina ta ce wa Manzon Allah (SAW) ya Manzon Allah! Shin in sanya maka wani abu wanda za ka rika zama a kansa? Lallai yarona masassaki ne. Ya ce, “In kin so,” sai ta yi masa mumbari. Lokacin da ranar Juma’a ta kasance sai Annabi (SAW) ya zauna bisa mumbari wanda aka aikata (ta yi) masa. Sai kututturen dabinon da (Annabi) ya kasance yana huduba a kansa ya yi kuka kamar zai tsage. Sai Annabi (SAW) ya suka ya kama shi ya rungume shi. Sai kututturen ya rika nishi (kuka) kamar kukan jariri (yaro) wanda ake rarrashi har sai da ya yi shiru. (Annabi) ya ce, “Ya yi kuka ne saboda abin da yake ji na wa’azi (huduba).”