Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 17

Babi na Hamsin da Shida: Cinikin abinci kafin karba da cinikin abin da ba shi a wurinka:584. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, abin da muka haddace shi daga Amru dan Dinar ya ji daga dawus yana cewa: “Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 17
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 17

Babi na Hamsin da Shida:
Cinikin abinci kafin karba da cinikin abin da ba shi a wurinka:
584. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, abin da muka haddace shi daga Amru dan Dinar ya ji daga dawus yana cewa: “Na ji dan Abbas (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Amma abin da Annabi (SAW) ya hana game da shi, shi ne: Cinikin abinci bai tabbata sai an karba.” dan Abbas ya ce, “Ban tsammanin komai kuma face misalinsa, hannu da hannu.”
585. An karbo daga Abdullahi dan Maslamta ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya sayi abinci kada ya sayar da shi face ya karbe shi bisa cikan ma’auninsa.” Isma’il ya kara da cewa, “Kada ya sayar da shi sai ya karbe shi.”

Babi na Hamsin da Bakwai:
Wanda ya ga idan mutum ya sayi abinci bisa bambi (tari) ba zai iya sayar da shi ba har sai ya dauke shi zuwa masaukinsa, ladabtarwa na ga wanda ya saba haka.
586. An karbo daga Yahya dan Kasir ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yunus daga dan Shihab ya ce, “Salim dan Abdullahi ya ba ni labari cewa: “Lallai dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Hakika na ga mutane a zamanin Manzon Allah (SAW) suna sayen abinci bambi (tari), ana dukansu idan suka sayar da shi a nan wurinsu kafin su tafi da shi zuwa Masaukinsu.”

Babi na Hamsin da Takwas:
Idan mutum ya sayi kaya ko dabba sai ya bar shi a wurin mai sayarwa, ko ya mutu kafin ya karba, (mene ne hukunci). dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Abin da ciniki ya kullu dabbar na da rai sai ta mutu tana bisa tsaron mai sayarwa mai saye shi ya yi asara.”
587. An karbo daga Farwata dan Abu Maghra’u ya ce: “Aliyu dan Mus’hir ya ba mu labari daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Yana da wahala a ce da wani yinin da Annabi (SAW) bai halarci gidan Abubakar ba da safe ko da yamma. Lokacin da aka yi masa izinin Hijira (kaura) zuwa Madina, ba mu ji tsoro ba face kamar ranar da ya zo mana da Azahar, sai aka ba Abubakar labari, sai ya ce, “Me ya kawo Annabi (SAW) a wannan lokaci face dai ko akwai wani abin da ya faru. Lokacin da ya shi gare shi ya ce, wa Abubakar fito da abin da ke gare ka na abinci.” Ya ce, “Ya Manzon Allah! Babu komai face yaran nan biyu, A’isha da Asma’u,” ya ce, “Na ji (an sanar da ni) game da fita (kaura).” (Abubakar) Ya ce, “Ina kaunar abuta da kai wurin tafiya ya Manzon Allah! Ya ce, “Abuta! Ya ce, “Ya Manzon Allah! Ina da rakuma biyu da zan yi tattalinsu domin fita sai ka karbi daya.” Sai (Annabi) ya ce, “Lallai zan karbe shi ne bisa kudi (ba kyauta ba).”

 Babi na Hamsin da Tara: An hana mutum ya yi ciniki bisa cinikin dan uwansa. Kuma kada ya yi tayi bisa tayin dan uwansa har sai ya yi masa izini, ko ya bar cinikin:

588. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada sashinku ya yi ciniki bisa cinikin dan uwansa (sashi).”