Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 18
Babi na Arba’in da Hudu: Idan ba a sanya lokacin zabi ba ga ciniki shin kasuwancin ya halatta?: 561. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari ya ce, Ayyuba ya ba mu labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Mai […]
Babi na Arba’in da Hudu: Idan ba a sanya lokacin zabi ba ga ciniki shin kasuwancin ya halatta?:
561. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari ya ce, Ayyuba ya ba mu labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Mai saye da mai sayarwa suna da zabin ciniki matukar ba su rabu ba, ko ya ce, “Face idan daya ya ce wa abokin cinikinsa zabi! Ko kuma (Annabi) ya ce, “Ko cinikin da aka yi bisa zabi.”
Babi na Arba’in da Biyar: Mai saye da mai sayarwa suna da zabin ciniki matukar ba su rabu ba. Da wannan dan Umar ya yi hukunci da Shuraih da Sha’abi da dawus da Adda’u da dan Abu Mulaikata:
562. An karbo daga Is’hak ya ce: “Habban dan Hilal ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari ya ce, kattada ya ce, daga Salih Abu Khalil daga Abdullahi dan Haris ya ce, “Na ji Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi) ya ce, daga Annabi (SAW) ya ce: “Mai saye da mai sayarwa suna da zabin ciniki matukar ba su rabu ba. Idan suka yi wa juna gaskiya suka bayyana aibi sai a sanya musu albarka. Idan suka yi wa juna karya suka boye aibi, sai a cire musu albarkar cinikinsu.”
563. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Masu ciniki biyu (mai saye da mai sayarwa) suna da zabin ciniki a tsakanin kowannensu matukar ba su rabu ba. Face cinikin da aka kulla bisa zabi.”
Babi na Arba’in da Shida: Idan mutum ya ba abokinsa zabin ciniki to lallai ciniki ya kullu (wajaba):
564. An karbo daga kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa daga Manzon Allah (SAW) cewa, lallai shi ya ce: “Idan mutum biyu suka yi ciniki kowane daya daga cikinsu na da zabi. Matukar ba su rabu ba, suna tare. Ko kuma idan dayansu ya ba daya zabin ciniki, to ciniki ya wajaba. Idan suka rabu a bayan sun kulla cinikinsu, kuma wani daga cikinsu bai bar cinikin ba, to lallai ciniki ya wajaba.”
Babi na Arba’in da Bakwai: Idan ya kasance mai saye ke da zabin ciniki shin cinikin ya halatta?:
565. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Abdullahi dan Dinar daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Dukkan ciniki bai kulluwa har mai saye da mai sayarwa sun rabu face cinikin da aka kulla bisa zabi.”