Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 19

Babi na Sittin da Hudu: Cinikin munabaza (jifa). Anas ya ce, Annabi (SAW) ya hana game da haka.: 595. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga Abu Zinad daga A’raji daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 19
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 19

Babi na Sittin da Hudu: Cinikin munabaza (jifa). Anas ya ce, Annabi (SAW) ya hana game da haka.:

595. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga Abu Zinad daga A’raji daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin mulasamatu (shafar tufafi) da munabaza (jifar tufafi).”

596. An karbo daga Ayyash dan Walid ya ce: “Abdul’a’alah ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Adda’u dan Yazid daga Abu Sa’id (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da sanya tufafi biyu, kuma ya hana game da ciniki biyu, mulasamatu (shafar tufa) da munabazat (jifar tufa).”

Babi na Sittin da Biyar:

An hana wa mai sayar da taguwa ko saniya ko tunkiya barin hantsarsu da nono domin yaudarar mai saye ya yi tsammani masu nono ne kwarai. Sai ya saye su da tsada:

597. An karbo daga dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ja’afar dan Rabi’ata daga A’araji ya ce, “Abu Huraira (RA) ya ce, “Daga Annabi (SAW) cewa: “Kada ku kyale hantsar taguwa ko tunkiya, don su yi tsada a kasuwa. Wanda duk ya sayi irin wadannan dabba bayan haka, to lallai na da zabin dayan abubuwa biyu idan ya riga ya tatse nononta ya sha (sa’an na ya bayyana masa yaudara ce). Idan ya so ya rike, idan ya so ya mayar da da ita da Sa’i daya na dabino ga mai sayarwa.” An ambato daga Abu Salih da Mujahid da Walidu dan Rabah da Musa danYassar daga Abu Huraira daga Annabi (SAW) cewa: “Sa’in daya na dabino, zai biya.” Wasu suka ce, daga dan Sirin ko kuwa: Sa’in daya na abinci, yana bisa zabin abubuwa uku.” Wasu suka ce, daga dan Sirin cewa: Sa’in daya na dabino bai ambaci zabin abubuwa uku ba, kuma babu maganar abinci, domin biyan dabino shi ya fi yawa.”

598. An karbo daga Musaddad ya ce: “Mu’atamir ya ba mu labari ya ce, “Na ji Babana yana cewa, “Abu Usman ya ba mu labari daga Abdullahi dan Mas’ud (RA), ya ce, “Wanda ya sayi akuya wadda aka bar hantsarta da nono domin ta yi tsada. Idan zai mayar da ita, to ya mayar da ita da Sa’i daya na dabino. Kuma Annabi (SAW) ya hana a rika taryar kaya daga masu sayarwa (saboda mai shi bai san farashin kasuwa ba, don haka zai sayar da arha).”

599. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (RA), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Kada ku rika taryar ayarin ’yan kasuwa. Kada sashi ya sayar wa sashi da kaya. Kuma kada ku rika ha’ici. Kada dan birni ya sayar wa mutumin kauye (a madadinsa). Kuma kada ku bar hantsar dabba da nono don ta yi tsada. Wanda ya saye ta, shi yana da zabin abubuwa biyu bayan ya sha nononta, idan ya so ya rike ta, idan ya ji zafi ya mayar da ita, da sa’i daya na dabino.”

Babi na Sittin da Shida: Wanda aka yaudara da barin hantsar dabba da nono idan ya sha nono yana iya mayar da ita da Sa’i daya na dabino:

600. An karbo daga Muhammad dan Amru ya ce, “Almakkiyu ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Ziyad ya ba ni labari cewa: Sabit bawan Abdurrahman dan Zaid ya ba shi labari cewa, lallai shi ya ji Abu Huraira (RA) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya sayi tunkiya mai nono cikin hantsarta kuma ya tatse nononta, idan ya yarda ya rike ta, idan ya yi fushi da ita, idan ya sha nononta, to, ya mayar da ita da Sa’i daya na dabino.”