Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi (20)
Babi na Tara: Ban ruwa har zuwa abinda yakai idon kafa:90. An karbo daga Muhammad ya ce: “Makhlad ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba ni labari ya ce, dan Shihab ya ba ni labari daga Urwata dan Zubair cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa: “Lallai wani mutumin Madina ya […]
Babi na Tara: Ban ruwa har zuwa abinda yakai idon kafa:
90. An karbo daga Muhammad ya ce: “Makhlad ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba ni labari ya ce, dan Shihab ya ba ni labari daga Urwata dan Zubair cewa: “Lallai shi ya ba shi labari cewa: “Lallai wani mutumin Madina ya yi husuma da Zubairu bisa wata magudanar ruwa a Harrat wanda ke ban ruwan dabino da ita. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka yi ban ruwan ya Zubair sai ya umarce shi da kyautatawa, sa’an nan ka sake ruwa zuwa ga makwabcinka. Sai mutumin Madina ya ce, “Don ya kasance dan Baffanka? Sai launin fuskar Annabi (SAW) ta canja sa’an nan ya ce, “Ka yi ban ruwan, sa’an nan ka tsare har ruwan ya komo zuwa ga bango (kago, ko katanga) har ya cika kogunan da ke tsakanin itatuwa. (Annabi) ya ba wa Zubairu hakkinsa. Sai Zubairu ya ce, “Wallahi lallai wannan aya ta sauka ne saboda haka, cewa: “A’a, ba za su yi imani ba face sai su sanya ka mai hukunci ga abin da ya faru a tsakaninsu…”(k:4:65). dan Shihab ya fada mini cewa da wannan ne, mutanen Madina da da sauran mutane suka rika kaddarawar maganar Annabi (SAW) cewa: Yi ban ruwa sa’n nan ka tsare har sai ya kai ga bango, haka din ya kasance gwargwadon tsawon idon kafa. Amma dai bango shi ne asalin.”
Babi na Goma: Fifikon shayar da ruwa:
91. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Summi daga Abu Salih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wata rana wani mutum yana tafiya sai kishirwa ya tsananta masa, sai ya sauka bisa wata rijiya ya sha daga gare ta, sa’an nan ya fita sai ya ga wani kare yana lallaga yana cin tabo mai damshi saboda kishirwa, sai ya ce: “Lallai wannan kare abin da ya same ni na kishirwa shi ma ya same shi, sai ya cika huffinsa sa’an nan ya kama shi da bakinsa, sa’an nan ya haye bisa domin ya shayar da karen, Allah Ya gode masa (mutumin) Ya gafarta masA.” Sai (Sahabbai) suka ce, “Ya Manzon Allah! Shin muna samun sakamako ta wajen dabbobi ne? Ya ce, “Haka yake ga dukkan dabba mai hanta danya wadda take kadawa (motsi) akwai sakamako.” Hammadu dan Salmata ya biye masa da Rabi’u dan Muslim daga Muhammad dan Ziyad.
92. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Nafi’u daga Abdulllahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “An taba azabtar da wata mace, saboda kyanwa (mage) da ta daure ta, har ta mutu saboda yunwa, sai ta shiga wuta saboda ita.” Ya ce, “Sai (Annabi) ya ce, “Allah Shi ne Mafi sani, (Allah) Ya ce, “Ke ba ki ciyar da ita ba, kuma ba ki shayar da ita ba, lokacin da kika daure ta, kuma ba ki sake ta, ta tafi ta ci daga ciyawar (abincin) kasa ba.”
Babi na Goma Sha daya: Wanda ke ganin cewa lallai mai tafki ko jakar fata na ruwa shi ke da hakkin amfani da ruwansa:
93. An karbo daga kutaiba ya ce: “Abdul’aziz ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi), ya ce; “An zo wa Manzon Allah (SAW) da wata buta (gora) sai ya sha daga cikinta, a gefen damarsa da wani yaro shi ne mafi karancin shekaru cikin mutane. Da kuma wasu dattawa a gefen hagunarsa (Annabi). Sai ya ce, “Ya kai yaro, shin za ka yi mini izini in bayar wa dattawan nan? Sai ya ce, “Ban kasance mai fifita kaina gare su a wajenka ba ya Manzon Allah, sai (Annabi) ya mika masa.”