Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 21

573. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Abu Damratu ya ba mu labari, ya ce, Musa ya ba mu labari daga Nafi’u ya ce: dan Umar ya ba mu labari cewa, lallai su sun kasance suna sayen abinci daga mahaya (ayarin matafiya) a zamanin Annabi (SAW), sai ya rika aikawa gare su da […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 21
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 21

573. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Abu Damratu ya ba mu labari, ya ce, Musa ya ba mu labari daga Nafi’u ya ce: dan Umar ya ba mu labari cewa, lallai su sun kasance suna sayen abinci daga mahaya (ayarin matafiya) a zamanin Annabi (SAW), sai ya rika aikawa gare su da wanda zai rika hana musu sayarwa inda suka saye shi sai sun dauko shi daga wurin sayar da abincin.” Ya ce:  “dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ba mu labari ya ce, “Annabi (SAW) ya hana sayar da abinci idan aka saye shi har sai ya karbe shi bisa cikawar ma’auninsa.”

Babi na Hamsin da daya: Abin da aka hana game da daga murya da karfi a kasuwa:

574. An karbo daga Muhammad dan Sinan ya ce: “Fulaihu ya ba mu labari daga Adda’u dan Yassar ya ce, “Na hadu da Abdullahi dan Amru dan Asi (Allah Ya yarda da su), sai na ce: “Ka ba ni labarin siffar Manzon Allah (SAW) a cikin Attaura,” ya ce, “Na’am zan ba ka labari, wallahi shi (Annabi) an bayar da siffarsa a cikin Attaura da wasu sashin siffofinsa a cikin Alkur’ani kamar haka: “Lallai Mun aiko ka, kana mai shaida kuma mai bishara mai gargadi. Kuma kana mai shiryarwa ga wadanda ba su iya karatu da rubutu ba. Kai bawaNa ne, kuma ManzoNa, Na sanya maka suna mai dogaro, ba mai bakar magana ba kuma ba mai kaurin fushi ba. Kuma ba shi saka mummuna da mummuna. Kuma ba mai daukaka murya a kasuwanni ba. Amma shi yana yafiya yana gafartawa. Allah ba zai karbi ransa face ya tsayar da addini wanda ya karkata daga bauta wa wani, don ku rika cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ana bude idanuwar makaho da ita, da kunnen bebe (kurma) da rufaffiyar zuciya.” Abdul’aziz dan Abu Salmata ya karbo daga Hilal, ya ce, “Sa’id ya ce daga Hilal daga Adda’u daga dan Salam.

Babi na Hamsin da Biyu:
Awo da gwajin kaya yana ga mai sayarwa ko mai ba da kyauta. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan za su gwada ko auna sai su rika tauyewa (83:3).” Yana nufin idan za su gwada wa wasu hatsi ko za su auna bisa sikeli kamar bisa fadarSa cewa: “Suna sauraronku, – da – fadin cewa, suna saurarawa gare ku. Annabi (SAW) ya ce, “Idan za ku karba daga hatsin awo kada ku kurba face bisa cikakken mudu.” An karbo daga Usman (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce masa: “Idan za ka sayar ka cika mudu, idan za ka auna ka bar mai sayarwa ya cika maka mudu.”

575. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya sayi abinci kada ya sayar da shi face sai ya wadatu da cikar ma’aunin daga wanda ya saya wurinsa.”

576. An karbo daga Abdan ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mughira daga Sha’abi daga Jabir (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abdullahi dan Amru dan Hiram ya mutu ana bin sa bashi, sai na nemi taimakon Annabi (SAW) bisa yafewar masu bin sa (Abdullahi) bashin, sai Annabi (SAW) ya nemi da su yafe masa, amma ba su yi haka ba. Sai Annabi (SAW) ya ce, mini ka tafi ka kasa dabinonka tari-tari (kaso daban-daban), dabinon Ajawa (na Madina mafi kyau) kashi guda, tari guda na dan Zaid daban, sa’an nan idan ka kare ka aika min. Sai na yi haka, sa’an nan na aika zuwa ga Manzon Allah (SAW), sai ya zo ya zauna bisa samansa ko tsakiyarsa, sa’an nan ya ce, “Auna ga mutanen, na auna musu har sai da na cika musu mudun kuma na biya bashinsu da suke bi. Kuma dabinona ya saura kamar ban rage komai ba daga gare shi.” Firas ya ce, daga Sha’abi ya ce, Jabir ya ba ni labari daga Annabi (SAW) cewa: “Jabir bai gushe ba yana auna musu har sai da ya biya bashinsa (Abdullahi).” Hisham ya ce, daga Wahab daga Jabir ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Yanke abin dabinon nan ka cika masa mudu.”