Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 22

Babi na Sittin da Bakwai:Sayar da bawa mazinaci. Shuraih ya ce, “Idan mai saye ya so yana iya mayar da shi ga mai sayarwa idan bawan ya kasance yana zina.” 601. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Sa’id Makburi ya ba ni labari daga Babansa daga […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 22
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 22

Babi na Sittin da Bakwai:
Sayar da bawa mazinaci. Shuraih ya ce, “Idan mai saye ya so yana iya mayar da shi ga mai sayarwa idan bawan ya kasance yana zina.”

601. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Sa’id Makburi ya ba ni labari daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa, lallai shi ya ji shi yana cewa: “Annabi (SAW) ya ce, “Idan baiwa ta yi zina kuma zinarta ta bayyana, sai shugabanta ya yi mata bulala kada ya zarge ta. Sa’an nan idan ta sake zina sai ya yi mata bulala kada ya zarge ta. Sa’an nan idan ta sake zina kashi na uku, sai ya sayar da ita, koda da igiya tubkakke na gashi.”

602. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi daga Abu Huraira da Zaid dan Khalid (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) an tambaya shi game da baiwar da take zina ba ta taba aure ba. Ya ce, “Idan ta yi zina sai shugabanta ya yi mata bulala, sa’an nan idan ta sake zina ya yi mata bulala. Sa’an nan idan ta sake zina ya sayar da ita ko da kudin tubkakken igiyar gashi.” dan Shihab ya ce, “Ban sani ba, a bayan ta uku ne, ko ta hudu ya ce, a sayar da ita.”

Babi na Sittin da Takwas: Saya da sayarwa tare da mata:
603. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwata dan Zubair cewa: A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya shiga gare ni, sai na ambata game da baiwa (Buraira). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ki saye ta ki ’yantata, domin kuwa lallai walicci yana ga wanda ya ’yanta ne.” Sa’an nan Manzon Allah Ya mike da yammaci ya yi wa Allah yabo da abin da ya dace da shi, sa’an nan ya ce: “Me ya sami mutane suna sharudda da abin da babu shi cikin Littafin Allah? Duk wanda ya yi wani sharadin da babu shi a cikin Littafin Allah, to batacce ne, koda ya yi sharudda dari ne. Sharadin Allah shi ne wanda ya fi cancanta kuma ya fi aminci.”
604. An karbo daga Hassan dan Abbad ya ce: “Hammam ya ba mu labari ya ce, na ji Nafi’u yana ba da labari daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta yi cinikin Buraira sai (Annabi) ya fito zuwa Sallah. Lokacin da ya zo sai ta ce, “Sun ki sayar da ita face sun shardanta da walicci.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Abin sani dai, lallai walicci yana ga wanda aka ’yanta.” Na ce, wa Nafi’u mijinta da ne ko bawa? Ya ce, “Me ya sanar da ni? Ban sani ba.”

Babi na Sittin da Tara:
Shin dan gari yana iya sayar wa mutumin kauye kaya ba tare da wani lada ba? Shin zai iya taimakonsa ko ya yi masa nasiha? Annabi (SAW) ya ce: “Idan dayanku zai yi wa dan uwansa nasiha to yana iya masa nasiha.” Adda’u ya yi rangwame game da haka.”

605. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufuyan ya ba mu labari daga Isma’il daga kaisu ya ce, “Na ji Jabir (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Na yi wa Manzon Allah (SAW) mubaya’a bisa shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne, da tsayar da Sallah da bayar da zakka, da ji da biyayya (ga dokokin Allah). Kuma da yin nasiha ga dukkan Musulmi.”