Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi (23)
Babi na Takwas: Hayar gona na noma bisa rabon rabin abin da aka samu da makamancinsa. kaisu dan Muslim ya ce daga Abu Ja’afar ya ce, “Babu wani gida daga gidajen masu hijira (kaura) face suna noma bisa ladar daya cikin uku, ko daya cikin hudu ga mutanen Madina. Aliyu da Sa’ad dan Malik da […]
Babi na Takwas:
Hayar gona na noma bisa rabon rabin abin da aka samu da makamancinsa. kaisu dan Muslim ya ce daga Abu Ja’afar ya ce, “Babu wani gida daga gidajen masu hijira (kaura) face suna noma bisa ladar daya cikin uku, ko daya cikin hudu ga mutanen Madina. Aliyu da Sa’ad dan Malik da Abdullahi dan Mas’ud da Umar dan Abdul’aziz da kasim da Urwat da Ali Abubakar da Ali Umar da Ali Aliyu da dan Sirin dukkansu sun yi aikin gona bisa wani rabo daga amfanin gona. Abdurrahman dan Aswad ya ce: “Na kasance ina tarayya da Abdurrahman dan Yazid a cikin wata gona. Umar ya sanya mutane aikin gona bisa cewa, idan Umar din ya gyara irin na da rabi. Idan su ne suka gyara irin suna da kamar kaza. Alhassan ya ce: “Babu laifi kasa ta kasance ga dayansu su ci gaba dayansu duk abin da ya fito nasu ne tare. Zuhuri ya ga haka daidai ne, Alhassan ya ce: “Babu laifi a debi auduga bisa rabon abin da aka samu biyu.” Ibrahim da dan Sirin da Adda’u da Alhakam da Zuhuri da kattada sun ce: “Babu laifi a bayar da auduga ga masaki bisa ladar daya cikin uku ko daya cikin hudu na tufafin da ya saka, ko da wani abu kamar haka.” Ma’amar ya ce, “Babu laifi kiwon dabbobi ya kasance bisa ga ladar daya cikin uku ko cikin hudu zuwa ajali sananne.”
62. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Nafi’u cewa: “Lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ba shi labari cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya sanya mutanen Khaibara bisa ga aikin gonakin dabino a kuma ladar rabin abin da aka samu daga ’ya’yan itace ko shuka. Sai ya kasance yana bayarwa ga matansa wasaki dari, wasaki tamanin na dabino, wasaki ashirin na sha’iri. Umar ya raba Khaibara ya bayar da zabi ga matan Annabi (SAW) bisa ga a yankan musu daga ruwa da kasa ko a bar su su ci gaba da aikinsu. Daga cikinsu akwai wadda ta zabi kasa, daga cikinsu akwai wadda ta zabi wasakin da (Annabi ke ba su kafin mutuwarsa). A’isha ta kasance daga wadanda suka zabi kasar.”
Babi na Tara: Idan mutum bai shardanta yawan shekaru ga mai haya ba, mene ne hukunci?:
63. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Ubaidullahi ya ce, Nafi’u ya ba ni labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce; “Annabi (SAW) ya sanya mutanen Khaibara bisa sharadin ladar rabin abin da aka samu daga ’ya’yan itace, ko shuka.”
Babi na Goma: Kamar abin da ya gabata:
64. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru ya ce, na ce, wa dawus cewa: “Da dai ka bar sana’ar mukhabarat (haya bisa rabon hatsi), saboda lallai mutane suna cewa: Annabi (SAW) ya hana game da haka. Ya ce, “Kai! Amru lallai ni, ina ba su hakkinsu kuma ina taimakonsu kuma wanda ya fi su sani ya ba ni labari wato dan Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Annabi (SAW) bai hana game da haka ba. Amma dai ya ce, “Abin da ya fi alheri ga dayanku shi ne ya bayar da gonarsa ga dan uwansa kyauta ba tare da sanya masa wani haraji ba.”
Babi na Goma Sha daya: Jingar aikin gona tare da Yahudawa:
65. An karbo daga dan Mukatil ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Ubaidullahi ya ba mu labari daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya bayar da Khaibara ga Yahudawa bisa ga jingar aikin gona a bisa ga shukarta amma suna da rabin abin da aka samu daga amfanin gona.”