Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 24
Babi na Hamsin da Uku: Abin da aka so game da cika mudu ko ma’auni: 577. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce, “Walid ya ba mu labari daga Sauri daga Khalid dan Ma’adan daga Mikdad dan Ma’ad Yakrib (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ku ci awon abincinku, sai […]
Babi na Hamsin da Uku: Abin da aka so game da cika mudu ko ma’auni:
577. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce, “Walid ya ba mu labari daga Sauri daga Khalid dan Ma’adan daga Mikdad dan Ma’ad Yakrib (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ku ci awon abincinku, sai a sanya muku albarka.”
Babi na Hamsin da Hudu: Albarkar Sa’in Annabi (SAW) da Muddinsa. Da wannan A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce, daga Annabi (SAW).
578. An karbo daga Musa ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Amru dan Yahya ya ba mu labari daga Abbad dan Tamim Ansari daga Abdullahi dan Yazid (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) cewa: “Hakika Ibrahim (A.S) ya haramta garin Makka, ya yi mata addu’a. To na haramta Madina da kamar yadda Ibrahim (A.S) ya haramta Makka, kuma na yi mata addu’a bisa Mudunta da Sa’inta, misalin abin da Ibrahim (A.S) ya yi ga Makka.”
579. An karbo daga Abdullahi dan Maslamta ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ya Allah! Ka sanya musu albarka a cikin ma’auninsu, kuma Ka sanya musu albarka a cikin Sa’insu, da Mudunsu, yana nufin mutanen Madina.”
Babi na Hamsin da Biyar: Abin da aka ambata a cikin kasuwancin abinci da boye abinci:
580. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Walid dan Muslim ya ba mu labari daga Auza’iyyu daga Zuhuri daga Salim daga Babansa (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ga wadanda suke sayen abinci bisa bambi (tari guda, ba tare da aunawa ba) a zamanin Manzon Allah (SAW) ana azabtar da su (bugunsu) idan suka sayar da shi kafin su tafi da shi zuwa masaukinsu.”
581. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari daga dan dawus daga Babansa daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya hana mutum ya sayar da abinci har sai ya karbe shi bisa cikkakken awo, kafin ya sayar da shi sai ya tafi da shi zuwa masaukinsa.” Sai na ce, wa dan Abbas, “Kamar yaya? Ya ce, “Dirhami da Dirhami, amma abinci bisa jinkiri har sai ya zamo bisa bayarwa hannu da hannu.” Abu Abdullahi ya ce, “Ma’anar murja’u shi ne: Wandanda ake jinkirtawa.”
582. An karbo daga Abu Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdullahi dan Dinar ya ba mu labari ya ce, Na ji dan Umar (Allah Ya yarda da su) yana cewa: “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya sayi abinci kada ya sayar da da shi face sai ya karbe shi.”
583. An karbo daga Aliyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya kasance yana ba shi labari daga Zuhuri daga Malik dan Ausu cewa: “Lallai shi ya ce, “Wa yake da kudin musanya (canji)? Sai dalhatu ya ce, “Ina da shi, amma sai mai tsaron taskar ya komo daga daji,” Sufiyan ya ce, “Shi ne muka haddace daga Zuhuri cewa, “Babu kari a cikin musanya,” sai ya ce, “Malik dan Ausu ya ba ni labari cewa, lallai shi ya ji Umar dan Khaddabi (Allah Ya yarda da shi), yana ba da labari daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Musanyar Zinari da Azurfa riba ce, face hannu da hannu (shi ne ba riba ba). Musanyar dabino da dabino riba ce, face hannu da hannu babu kari. Musanyar Sha’iri (alkama) da Sha’iri riba ce, face hannu da hannu babu jinkiri ba kari.”