Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 25

589. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Zuhuri ya ba mu labari daga Sa’idu dan Musayyib daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya hana mazaunin gida ya sayar wa mutumin kauye kaya (a madadinsa). Kuma ya ce, kada ku rika neman mai saye […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 25
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 25

589. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Zuhuri ya ba mu labari daga Sa’idu dan Musayyib daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya hana mazaunin gida ya sayar wa mutumin kauye kaya (a madadinsa). Kuma ya ce, kada ku rika neman mai saye da mayar da kaya ga mai sayarwa. Kuma kada mutum ya yi ciniki bisa cinikin dan uwansa. Kada dayanku ya yi neman aure bisa neman auren dan uwansa. Kuma kada mace ta nemi sakin ’yar uwanta don ta maye wurinta.”

Babi na Sittin: Ciniki bisa kari (gwanjo). Adda’u ya ce, “Na iske mutane ba su ganin laifi cinikin kayan ganimomi bisa kari (gwanjo)”:

590. An karbo daga Bishiru dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Alhusain Muktab ya ba mu labari daga Adda’u dan Abu Rabah daga Jabir dan Abdullahi (RA) cewa: “Lallai wani mutum ya ’yanta wani saurayi (yaronsa) bisa dubur (bayan mutuwa) daga baya sai ya kasance mabukacin kudi. Sai Annabi (SAW) ya karbe shi ya ce, “Wane ne zai saye shi daga wurina? Sai Nu’aimu dan Abdullahi ya saye shi da kaza-da– kaza, sai ya mika shi gare shi.”

Babi na Sittin da daya:
Najashu (ha’incin komai a ciniki). Bisa fahimtar wanda ya ce, “Wannan ciniki ba shi halatta,” dan Abu Awfa ya ce, “Mai halin najashi, maciyin riba ne, kuma maha’inci ne. Shi ne mummunar yaudara, kuma batacciya ba ta halatta.” Annabi (SAW) ya ce, “Yaudara tana wuta, wanda ya aikata wani aiki wanda babu shi cikin al’amarinmu, to, an mayar (ba a karba ba).”

591. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Malik ya ba mu labari, daga Nafi’u daga dan Umar Allah (RA), ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da najashi (yaudarar ciniki).”

Babi na Sittin da Biyu: Cinikin garari (abin da babu shi a hannu, kamar sayen biri a sama) da cinikin dan cikin dabba:

592. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar Allah (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hana game da sayar da dan cikin dabba tun ba haife shi ba. Saboda ciniki ne da ya kasance mutane Jahilyya suke yin sa. Mutum zai kasance yana sayen dan cikin taguwa har zuwa ta haife abin cikinta ta shayar da shi.”

Babi na Sittin da Uku: Cinikin shafar tufafi kafin budewa. Anas ya ce, “Annabi (SAW) ya hana game da haka”:

593. An karbo daga Sa’id dan Ufair ya ce: “Laisu ya ba ni labari ya ce, Ukailu ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce, Amir dan Sa’ad ya ba ni labari cewa: “Lallai Abu Sa’id (RA), ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya hana game da cinikin munabaza (shi ne mutum ya jefa maka tufafinsa kai ma ka jefa masa taka bisa ciniki tun kafin ya bude ko ya yi dubi gare shi). Kuma ya hana game da cinikin mulasamatu (shi ne shafar tufafi amma ban da dubawa gare shi).”

594. An karbo daga kutaiba ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, Ayyub ya ba mu labari daga Muhammad daga Abu Huraira (RA) ya ce, “(Annabi) ya hana game da dauri (sanya) tufafi biyu. Shi ne mutum ya lulluba cikin tufafi daya, sa’an nan ya kwashe ya zuba bisa kafadarsa. Kuma ya hana game da ciniki biyu, Limmas (shafa) da Nubaz (jifa).”