Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 5
Babi na Hamsin da Shida: Azumin lokaci (kullum): 436. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id dan Musayyab ya ba ni labari da Abu Salmata dan Abdurrahman cewa: “Lallai Abdullahi dan Amru dan Asi (Allah Ya yarda da su), ya ce, “An ba Manzon Allah […]
Babi na Hamsin da Shida: Azumin lokaci (kullum):
436. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id dan Musayyab ya ba ni labari da Abu Salmata dan Abdurrahman cewa: “Lallai Abdullahi dan Amru dan Asi (Allah Ya yarda da su), ya ce, “An ba Manzon Allah (SAW) labarin cewa, lallai ni, ina fadin cewa: Wallahi zan rika azumin yini kuma wallahi zan kwana nafilar dare matukar ina raye. Sai na ce, masa na fade shi (kamar haka). Babana da Mahaifiyata fansa ne gare ga ya Manzon Allah! Ya ce, mini “Ba za ka iya aikata haka ba, ka yi azumi kuma ka ci washegari. Ka yi nafilar dare kuma ka yi barci, kuma kana iya azumin kwana uku kowane wata domin lallai kowane aiki mai kyau da sakamakon goma misalinsa, wannan ya zamo kamar azumin lokaci duka.” Na ce, “Lallai ina da ikon yi fiye da haka,” sai ya ce, “Ka yi azumi yini daya ka sha ruwan kwana biyu,” na ce, “Ina da ikon yin fiye da haka,” ya ce, “Ka yi azumin yini gobe ka sha ruwa, wannan shi ne azumin Dauda (AS).” Sai na ce, “Ina da ikon yi fiye da haka,” sai (Annabi) ya ce, “Babu wani azumi fiye da haka.”
Babi na Hamsin da Bakwai: Hakkin iyalai a cikin azumin nafila. Abu Juhaifa ya ruwaito shi daga Annabi (SAW):
437. An karbo daga Amru dan Aliyu ya ce: “Abu Asim ya ba mu labari daga dan Juraij ya ce: “Na ji Adda’u ya ce, lallai Abu Abbas mawaki ya ba shi labari, cewa: “Lallai shi ya ji Abdullahi dan Amru (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Labari ya isa ga Annabi (SAW) cewa, “lallai ni ina azumi kullum, kuma ina kwana Sallar Dare. Da dai na hadu da shi sai ya ce, “Shin an ba ni labari cewa, “Lallai kai kana azumi ba ka shan ruwa kuma kana Sallar Dare kullum? To ka yi azumi yini gobe ka sha ruwa, ka yi Sallah kuma ka yi barci. Domin lallai idonka na da rabon hakki gare ka, kuma ranka da iyalanka suna da rabon hakki a gare ka.” Abdullahi ya ce, “Lallai ina iya fiye da haka,” (Annabi) ya ce, “Ka yi azumi irin azumin Dauda (A.S), sai ya ce, “Kamar yaya? Ya ce, “Ya kasance yana azumin yini gobe ya sha ruwa, kuma ba shi gudun abokan gaba idan suka hadu.” Ina zan samu wannan lokaci ya Annabin Allah? Adda’u ya ce, “Ban san yadda ya ambaci azumin kullum ba? Annabi (SAW) ya ce, “Babu azumi ga wanda yake azumin kullum, (ya fada) har sau biyu.”
Babi na Hamsin da Takwas: Azumin yin gobe a sha ruwa:
438. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce, “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’aba ya ba mu labari daga Mughirah ya ce, “Na ji Mujahid ya karbo daga Abdullahi dan Amru (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Ka yi azumin kwana uku kowane wata,” ya ce, “Ina iya fiye da haka, bai gushe ba har sai ya ce, “Ka yi azumin yini, gobe ka sha ruwa.” Ya ce, “Ka karanta Alkur’ani a cikin kowane wata.” Ya ce, “Ina iya fiye da haka bai gushe ba na fadin haka har sai da ya ce, “Ka karanta cikin kwana uku.”