Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 6
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi Babi na Hamsin da Tara: Azumin Dauda (AS): 439. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce, Habib dan Abu Sabit ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Abbas Al-makkiyu ya kasance mawaki ne, kuma ya kasance ba a tuhumarsa cikin hadisinsa ya […]
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus
Almashgool, Bauchi
Babi na Hamsin da Tara: Azumin Dauda (AS):
439. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari ya ce, Habib dan Abu Sabit ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abu Abbas Al-makkiyu ya kasance mawaki ne, kuma ya kasance ba a tuhumarsa cikin hadisinsa ya ce, “Na ji Abdullahi dan Amru dan Asi (RA), ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya fada mini cewa: “Lallai kai kana azumin kullum ko, kuma kana tsayuwar dare dukkansa?” Na ce, “Na’am,” ya ce, “Lallai kai idan kana aikata haka, idonka zai rauni kuma jikinka zai gajiya. Babu azumi ga wanda yake azumin kullum, ka yi azumin kwana uku a matsayin azumi kullum yake.” Na ce, “Ina iya fiye da haka.” Ya ce, “Ka yi azumi irin azumin Dauda (AS), ya kasance yana azumin yini, gobe ya sha ruwa, kuma ba shi gudu idan ya hadu da abokan gaba.”
440. An karbo daga Is’hak dan Shahi Alwasidiyyu ya ce: “Khalid dan Abdullahi ya ba mu labari daga Khalid Haza’u daga Abu kilabata ya ce, “Abu Malih ya ba ni labari ya ce, “Na shiga tare da Babanka Abdullahi dan Amru sai ya ba mu labari cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) an ba shi labari game da yawan azumina. Sai ya shigo gare ni wata rana na jefa masa matashi na fata wanda aka cika da tufkakken kaba, sai ya zauna a bisa kasa, sai matashi ya kasance tsakanina da shi. Sai ya ce, “Shin ba zai ishe ka ba, ka rika yin azumin kwana uku kowane wata? Ya ce, “Na ce, “A’a, ya Manzon Allah!’ Ya ce, “Biyar fa.” Na ce, ‘A’a, ya Manzon Allah!’ Ya ce, “bakwai fa.” Na ce “A’a ya Manzon Allah’ Ya ce, “Tara fa.” Na ce, “A’a, ya Manzon Allah! Ya ce, “Goma sha daya fa.” Sa’an nan Annabi (S.W) ya ce, “Babu azumi sama (fiye) da azumin Dauda (A.S), rabin zamani, ka yi azumin yini, gobe ka sha ruwa.”
Babi na Sittin: Azumin kwanaki zababbu su ne:(13 da 14 da 15 ga wata ):
441. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdul Waris ya ba mu labari ya ce, Abu Tiyah ya ba mu labari ya ce, “Abu Usman ya ba ni labari, daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Masoyina ya yi mini wasiyya da abubuwa uku: (1) Azumin kwana (yini) uku cikin kowane wata. (2) Raka’a biyu na walha. (3) Yin sallar wutiri kafin in yi barci.”
Babi na Sittin da daya: Wanda ya kai ziyara ga wasu mutane a cikin azumi amma bai yi buda baki a wurinsu ba:
442. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Khalid dan Haris ya ba mu labari ya ce, Humaid ya ba mu labari daga Anas (RA) cewa: “Wata rana Annabi (SAW) ya shiga wurin Ummu Sulaim sai ta zo masa da dabinai da mai (cuku). Sai ya ce, “Ku koma da dabinanku da manku cikin mazubinsa da tandunsa (wurin ajiya), domin hakika ina azumi.” Sa’an nan ya tsaya daga wani bangaren daki (gidan) ya yi Sallah wadda ba ta farilla ba, ya yi wa Ummu Sulaimin addu’a da iyalan gidanta. Sai Ummi Sulaimi ta ce, “Ya Manzon Allah! Ina da wata bukata.” Ya ce, “Mece ce? Ta ce, “Mai aikinka Anas, nake nufi, bai bar wani alherin lahira ko na duniya ba face ya rokan mini (Allah) shi. Ya ce, “Ya Allah! Ka azurta shi da dukiya da ’ya’ya kuma Ka sanya masa albarka.” (Anas) ya ce, “Lallai na kasance wanda ya fi mutanen Madina dukiya.” ’Yata ta ba ni labari cewa, Umainah dan cikina lallai shi an bisne shi a lokacin gabatar Hajjaju a Basara da kamar shekara dari da Ashirin da wani abu.” dan Abu Maryam, ya ce, Yahya dan Ayyub ya ce, Humaid ya ba ni labari ya ce, “Na ji (daga) Anas (RA) daga Annabi (SAW).”