Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 7

Babi na Hamsin da daya: Wanda ya yi rantsuwa ga dan uwansa don ya karya azumin nafila. Kuma babu biya a kansa idan ya yi masa biyayya ga karya azumin: 428. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ja’afar dan Aunu ya ba mu labari, ya ce, Abu Umaish ya ba mu labari daga […]

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 7
Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 7

Babi na Hamsin da daya: Wanda ya yi rantsuwa ga dan uwansa don ya karya azumin nafila. Kuma babu biya a kansa idan ya yi masa biyayya ga karya azumin:

428. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ja’afar dan Aunu ya ba mu labari, ya ce, Abu Umaish ya ba mu labari daga Aunu dan Abu Juhaifa daga Babansa ya ce, “Hakika Annabi (SAW) ya hada zumuntar ’yan uwanta a tsakanin Salman da Abu Darda’u. Sai Salman ya ziyarci Abu Darda’u ya ga Ummu Darda’u a cikin tufafi mara kayatarwa, sai ya ce, mata: “Mene ne sha’aninki (me ya faru da ke)? Ta ce, “dan uwanka Abu Darda’u ne ba shi da wata bukata game da duniya. Sai Abu Darda’u ya zo ya yi masa abinci, (Salman) ya ce, “Ka ci, ya ce, “A’a ni ina azumi,” ya ce, “To ni, ba zan ci ba har sai ka ci.” Ya ce, “Sai ya ci, lokacin da dare ya yi, sai Abu Darda’u ya mike domin nafilar dare,” Sai (Salman) ya ce, “Kwanta ka yi barci, ya yi barci sa’an nan ya ta shi domin nafila, sai (Salman) ya ce, “Kwanta dai ka yi barci.” Lokacin da karshen dare ya kasance, sai Salman ya ce: “Tashi yanzu ka yi nafilar dare, sai suka yi Sallah.” Salmanu ya ce, masa: “Lallai Ubangijinka na da hakki a kanka, ranka na da hakki a kanka, iyalanka na da hakki a kanka, ka rika ba da mai hakki hakkinsa.” Sai (Abu Darda’u) ya tafi ga Annabi (SAW) ya ambata masa labarinsa (Salman), sai Annabi (SAW) ya ce, “Salmanu ya yi gaskiya.”

Babi na Hamsin da Biyu: Azumin watan Sha’aban:

429. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Nadir daga Abu Salmana daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har mu rika cewa, bai cin abinci. Kuma yana zama bai azumi har mu rika cewa ba zai yi azumin ba. Amma ban ga Manzon Allah (SAW) ya cika azumin wata daya ba face Ramadan. Kuma ban ga inda ya fi yawaita azumi ba kamar a cikin Sha’aban.”

430. An karbo daga Mu’az dan Faddala ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Yahya daga Abu Salmata cewa: “Lallai A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce, “Annabi (SAW) bai kasance yana yawaita azumtar wani wata ba face watan Sha’aban. Kuma ya kasance yana cewa: “Ku riki aikin da kuke iyawa, domin Allah ba Ya kosawa har sai kun kosa.” Kuma sallar da Annabi (SAW) ya fi so wadda aka dauwama a kanta komin karancinta. Kuma ya kasance idan zai yi sallar nafila yakan dauwama kanta.”

Babi na Hamsin da Uku: Abin da aka ambata game da azumin Annabi (SAW) da cin abincinsa:

431. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awanata ya ba mu labari daga Abu Bishiru ya ba mu labari daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (RA) ya ce, “Annabi (SAW) bai taba yin azumin wata daya cikakke ba, face Ramadan. Kuma yana azumi har mai magana yakan ce, “A’a, wallahi ba zai ci ba. Kuma yana zama ba ya azumi har mai magana na cewa: “A’a, wallahi ba zai yi azumi ba.”